Wadansu Matasa Sun Yi Wa Hukumar KASTELEA Zanga-Zanga A Kaduna

0
750
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

WADANSU matasan da suke haya da motocin Bus da kuma zauna Gari banza da ke kokarin bijirewa dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa a kan hukumar KASTELEA masu aikin kiyaye dokokin hanya a duk fadin jihar na kokarin mayar da hannun agogo baya.
Su dai matasan kamar yadda wakilinmu ya ji ta bakin su na korafin cewa jami\’an hukumar KASTELEA da ke kula da dokokin  tukin ababen hawa suna matasa masu domin ayyukan yau da kullum.
\”A gaskiya muna samun matsi kwarai daga ma aikatan hukumar KASTELEA domin yawan tarar da ake karba ya yi yawa, shi ya sa muke kokarin yin wannan zanga-zanga\”.
Su dai matasan na sauke mutane fasinjojin motoci ne na Keke Napep da motocin Bus suna kuma tilasta su saka ganye a motocinsu.
Amma a ta bakin wasu fasinjojin da aka suke na korafin an yi masu zaluncin hana su kudin su bayan an tilasta su sauka daga ababen hawan da suka dauko su zuwa wuraren da za su.
Su dai jami\’an hukumar KASTELEA dokar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ce ta kafa su domin kula da dokokin hanya ga wanda ya karya kuma akwai hukunci, an kuma dauki lokaci a wayar wa da jama a kai game da ayyukan hukumar.
Wakilinmu na kokarin jin ta bakin mahukuntan hukumar ko bangaren gwamnatin wanda ya zuwa yanzu duk al\’amarin ganin haka ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here