Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNAN jihar Imo Cif Rochas Okorocha ya ce babu mutum daya daga cikin gwamnonin ko sarakunan kabilar Igbo ta kudu maso gabashin Nijeriya da ke goyon bayan fafutukar kafa kasar Biafra.
Kiraye-kirayen a ware da kuma zargin rashin adalci a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari da wasu \’yan kabilar ta Igbo ke yi na karuwa a kasar.
Ko a kwanakin baya ma, sai da shugaban kungiyar MOSSOB,mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya yi wani gangami inda ya jaddada kiran warewa daga Najeriya.
A wata hira da manema labarai , Cif Okorocha Gwamnan jihar Imo a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda kungiyar take ya ce da farkon fari ma batun cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na nuna banbanci bai taso ba.
Gwamna Okorocha ya ce babu zancen cewa ba a damawa da \’yan kabilar Igbo a gwamnatin kasar, kodayake ya akwai bukatar a kara jan \’yan kabilar tasa a jiki.
\’\’ Ai muna da ministoci, muna da wasu da ke kan wasu manyan mukamai, akwai abubuwan da ya kamata gaskiya a duba, bai kamata a ce ba a yi da Ibo ba.\’\’
Ya kamata Buhari ya duba kalaman matarsa.
Cif Okorocha ya ce in dai batun mukamai ne a wasu lokutan akwai abubuwan da ake dubawa ba wai kawai batun kabilanci ba. Ya kuma kara da cewa ;
\’\’ Misali kamar yadda aka bayar da mukaman manyan hafsoshin sojin kasar, an yi la\’akari da matsalar Boko Haram kan me za a yi don samun wanda zai shawo kan matsalar.\’\’
Kan batun da ake yi cewa gwamnonin yankin kudu maso gabashin Nijeriyar na mara wa Nnamdi Kanu baya a fafutikar da yake yi ta kafa kasar Biafra, Gwamna Rochas Okorocha ya musanta da cewa sam hakan ba gaskiya ba ne.
\’\’Tambayata a nan ita ce, kana ganin a zama na na Rochas haka, sai Nndamdi Kanu zai zo ya kira ni yaki kuma in bi shi?, Ka san ba mai yiwuwa ba ne\’\’, babu wani Gwamna ko Basarake a kudu maso gabashin Nijeriya da ke goyon bayan Ndamdi Kanu da fafutikar da yake yi ta raba Nijeriya.\’\’ in ji Rochas.
Nnamdi Kanu ya kafa kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, wadda take farfado da batun kafa Biafra
Gwamna Okorocha ya ce batun raba Nijeriya \’yan kabilar Ibo su ware abu ne da hankali ba zai dauka ba.
\’\’Wai shin Nnamdi Kanu wane ne shi a cikin kabilar Ibo?, Kuma idan aka raba Nijeriya a kai ta ina?