Dan Daudu Mai Shigar Mata Don Yaudarar Maza Ya Shiga Hannu

0
799
Daga Usman Nasidi
AN kama wani katoton gardi da ya shahara wajen yin shigar mata domin yaudarar maza, kuma zakara na ba shi sa’a yana samun nasara, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Majiyarmu ta samu labarin tabbacin wannan matashi ya sha karbar kudaden samari sanadiyyar wannan shigar a cuci maza da yake yi.
An ruwaito wanann matashi yakan yaudari maza ne ta hanyar tsayawa a gefen titi, inda yake tsayar da motoci musamman motocin gayu domin a rage masa hanya, daga nan ne fa sai ya fara tattausa murya kamar macen gaske.
Daga karshe wannan matashi ya bayyana yadda yake fara samun dama a kan mazan shi ne ta hanyar lambar wayoyinsu, daga baya sai ya ci gaba da yaudarar wawaye daga cikin maza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here