Daga Usman Nasidi
WATA mai sayar da soyayya ta soka wa wani dan kasuwa kwalba wanda hakan ya yi sanadiyyar tafiyarsa lahira a wani sannanan Otel da ke kusa da Abraka Quarters a garin Asaba da ke jihar Delta bisa dalilin rashin biyan ta kudin sayar da soyayar.
Wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin a otel din, hakan kuma ya haifar da tashin hankali saboda mazauna unguwar ba su taba tsamanin mai siyar da soyayyar za ta aikata hakan ba.
Jami’an \’yan sanda da suka yi magana da manema labarai amma sun nemi a sakaya sunansu sun ce mai siyar da soyayyar ta tare dan kasuwan ne a lokacin da yake ketarowa daga gadar Niger sannan ta daba mishi kwalba bisa dalilin rashin biyan ta da bai yi ba.
Wadanda abin ya faru a idon su sun ce wadda ake zargi da kisan ta tare dan kasuwan ne wanda take zargin ya sha mugan kwayoyi wanda hakan ne ya sa ya wuce lokacin da ta diba masa, hakan kuma bai yi mata dadi ba shi ya sa ta nemi ya kara mata kudi.
Bayan ya ki ya kara mata kudin, sai ta fito da kwalba, ta fasa kwalbar sannan ta daba masa a ciki, ta yi tafiyarta ta bar shi cikin jini sannan daga bisani jami’an tsaro suka shigo otel din.
Wani dan sanda da bai son a fadi sunansa da ke shelkwatan \’yan sanda na jihar ya tabbatar da cewa wadda ake zargi tana tsare domin \’yan sanda su ci gaba da bincike.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun rufe otel din, shi kuma Manaja da sauran ma’aikata sun tsere domin tsoron abin da zai biyo baya.