Ya Amsa Laifinsu Ne Matsalolin Da Arewacin Kasar Nan Ke Ciki A Halin Yanzu

0
809

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MAI alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa\’ad Abubakar na uku ya tabbatar wa da duniya cewa duk matsalolin da ke addabar arewacin Nijeriya Laifinsu ne magabata da suka haifar da su tun da dadewa.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bude taron sarakuna da gwamnonin arewacin kasar da ke gudana a gidan gwamnatin Jihar Kaduna.
\”Kasancewar faruwar hakan ya dace mu da muka haifar da wadannan matsalolin mu tashi tsaye domin ganin mun warware su baki daya,kuma ya zama wajibi mu guji furta kalaman da za su haifar wa kasa matsaloli domin abu ne mai sauki ka furta kalamai amma ba a san abin da za su haifar ba\”.
Ya kuma ci gaba da karin hasken cewa za su duba ko an samu wani ci gaba a taron da suka yi da Gwamnonin irin wannan watanni shida baya domin a san inda aka fuskanta wanda ta haka ne za a samu nasarar da ake bukata.
A jawabansu daban-daban mai masaukin baki Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i da kuma wakilin shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin kasar Kashim Shatima wanda yake kasar Ingila domin gudanar da wadansu muhimman ayyuka da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya wakilta a wajen bude taron duk sun yi jan hankali ne a cikin jawabai masu tsawo bisa irin yadda za a warware matsalolin da yankin ke fuskanta. Fata dai a samu ci gaba a taron da suka kulle dakin taron suna tattaunawa a tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here