Mustapha Imrana Abdullahi Daga kaduna
KWAMISHINAN kula da ma\’aikatar gona da albarkatun gandun daji na Jihar Kaduna Furofesa Kabiru Mato, ya bayyana muhimman dalilan da suka haifar wa Jihar karkashin Nasiru Ahmad El-Rufa\’i daina bayar da tallafin sayar da takin zamani.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce hakika lokaci ya wuce da gwamnati za ta rika amfani da dukiyar jihar domin noma.
\”Saboda haka za a sama wa masu son zuba jari ingantaccen yanayin da za su gudanar da harkokinsu ta yadda za su samu amfani sosai\”.
Ya kara da fayyace cewa idan mutum ya saya kuma ya bayar da tallafin takin zamani zai zama wani lamari na harkar siyasa, ko kuma harkar kungiyoyi masu zaman kansu, don haka ba mu sayen takin zamani a madadin hakan muna kokarin samawa masu son hada kamfanin in hada takin zamani ta yadda za su samu zuwa Jihar Kaduna su Kuma sayar da Takin zamani a kan Fara shin da aka kayyade na dubu biyar da dari biyar ,ga manoma na gaskiya kamar yadda muka bincika kuma muka san su\” duk wadannan kalamansa ne kamar yadda ya yi su.
\”Don haka ba mu bukatar yin kasafin kudi na biliyoyin naira domin sayo takin zamani a madadin hakan za mu ware \’yan kudi kalilan ne domin biyan kudin daga cikin birnin Kaduna ko duk inda aka ajiye takin zuwa sauran sassan Jihar kaduna. don haka a batu na gaskiya bayar da tallafin takin zamani lamari ne kawai na siyasa Amma ba ci gaba ba\”. Inji shi.
Mato ya ci gaba da cewa a Jihar Kaduna suna tafiyar da harkar noma a matsayin wani aiki ga jama a saboda haka muna yi ne a matsayin kasuwa ci domin masu kokarin zuba jari su samu yanayi mai kyau, don haka ba wai zamu yi amfani da dukiyar jama\’a ayi harkar noma amma muna amfani da dukiyar jama\’a ne domin samar da domin masu zuba Jari na ciki da wajen jihar har ma da kasashen waje su zo da dukiyar su ta yadda za su bunkasa harkar noma\”kamar yadda Mato ya gaya wa manema labarai.
\”Zai zamo wani kuskure kwarai mu ci gaba da yin abin da ake yi tun shekarun baya can a kan harkar noma domin mun ga lamarin bai haifar da da mai idanu ba domin kowa ya sani yanayin bai taimaka wa kowa ba a fadin jiha.
A game da batun gandun daji kuma, Mato ya ce dokokin da suke a wannan bangare hakika sun yi rauni saboda haka gwamnati na kokarin kara inganta su ta yadda za su zama masu karfi domin hana masu al\’adar shiga dazuzzuka jihar suna sare itatuwa ba gaira ba dalili.
Don haka kwamishinan yake kira ga dimbin jama\’a bdaki aya su kula kada su sake su shiga cikin dajin da gwamnati ta ware saboda duk Wanda aka samu doka za ta yi aiki a kan sakamakon.