Na Rantse Da Kur\’ani Ne Domin In Wanke Kaina – Adam Zango

0
974

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SANANNEN dan fim din Hausa Adam A Zango ya bayyana cewa ya dauki Al-kur\’ani ne ya rantse domin wanke kansa daga zargin yin luwadi.
\”Ni a gaskiya ina matukar tsanar wani ya ce  da ni dan luwadi saboda ko mutuwa na yi za a iya kiran dana ubansa dan luwadi ne don haka na tsani a kira ni dan luwadi, shi ya sa na dauki Al-kur\’ani a kaina na rantse domin in wanke kaina\”.inji Zango
Ya kuma bayyana hakan ne a cikin wata hirar da ya yi da gidan rediyon BBC mai yada shirye-shiryensa a sashin Hausa.
\”Na je ma neman aure amma an je an kai suka ta cewa ni dan luwadi ne wanda kuma ba haka ba ne\”.
Ya bayyana cewa duk da ya taba auren \’yar fim sun rabu har gobe zai iya auren macen da ke yin fim.
Ya ce shi ya sa ya rantse domin shi bai taba yi da wani ba kuma ba a taba yin luwadi da shi ba ko kadan.
A game da batun dakatar da \’yar wasan fim Rahama Sadau ya bayyana lamarin da cewa akwai wasu da ba za a iya dakatar da su ba, domin ko an ce an dakatar da wasu sai dai a yi na wani dan wani lokaci kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here