AN CI GÀBA DA CIYARWA A MAKARATUN FIRAMARI A JIHAR KADUNA

0
833
Daga Usman Nasidi
SHIRIN ciyar da dalibai \’yan makaranta na gwamnatin tarayya ya kankama a jihar Kaduna, inda a ranar Litinin 31 ga watan Yuli za’a ciyar da dalibai sama da 800,000.
Darakta a ma’aikatan ilimi na jihar Kaduna, John Gora ne ya tabbatar ma majiyar NAIJ.com wannan labari, inda yace gwamnatin jihar zata kashe naira miliyan 56 a duk rana, da kuma naira biliyan 1.1 a duk wata. Haka zalika Gora yace masu aikin girki 9,000 kacal za’a iya dauka a yanzu.
“Kamar yadda aka tsara, gwamnatin tarayya zata ciyar da yan aji 1-3, yayin da gwamnatin jiha zata ciyar da yan aji 4-6, amma idan ba’a manta ba, a bayan da aka fara shirin a jihar Kaduna, gwamnatin jiha kadai ke ciyar da dukkanin daliban.
Yan makarantun Firamari.
“Ka ga kenan gwamnatin jihar ta dauke ma gwamnatin tarayya nauyi a baya, kuma kudaden da jihar ke bin gwamnatin tarayya a dalilin haka sun kai naira biliyan 7, a yanzu gwamnatin tarayya ta biya jihar Kaduna naira biliyan 3.5.” Inji Gora.
Sai dai yace da zarar gwamnatin tarayya ta kammala biyan gwamnatin jiha kudadenta, za’a ci gaba da ciyar da yan aji 4-6, sa’annan sakamakon wannan gibin da aka samu, iya ma’aikatan girki 9,000 kacal za’a iya dauka daga cikin 20,146 da suka nema har sai an biya sauran kudaden.
A wani labarin kuma, shugaban gudanar da aikin ciyarwar na gwamnatin tarayya, Adebayo Dotun, ya ce sun horar da jami’ai 200 da zasu sanya idanu don tabbatar da samun nasarar shirin, ta hanyar tabbatar da tsafta da ingancin abincin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here