BABBAN BURINMU TALAKAN NIJERIYA YA SAMI ‘YANCI-KWAMARED BASHIR DAUDA

    0
    949
     Isah Ahmed, Jos
     
    A makon da ya gabata ne tawagar shugabannin  kungiyar muryar talaka ta kasa, karkashin jagorancin sakataren kungiyar na kasa  Kwamared Bashir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina ta kawo ziyara ga reshen kungiyar na jihar Filato. A tattaunawarsa da  wakilinmu kan burin wannan kungiya,  sakataren kungiyar  ya bayyana cewa babban burin  kungiyar shi ne ta ga cewa talakan Nijeriya ya sami \’yanci kuma Nijeriya ta gyaru.
     
    Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
     
    GTK: A wane lokaci ne aka kafa wannan kungiya kuma mene ne mafufofinta?
     
    Kwamared Bashir Dauda: Mun fara tunanin kafa wannan kungiya ne a shekara ta 2003. Wato a lokacin da aka fara samun ci gaba ta bangaren sadarwa a nan Nijeriya musamman hanyar sadarwar yanar gizo.
    A lokacin akwai kafofin watsa labarai na kasashen waje kamar BBC Hausa da Muryar Amurka da Sashin Hausa na muryar Jama’ar Jamus da Rediyo China suka fara ba da dama ga masu sauraronsu, su rika tura  wasiku da ra’ayoyi ana karantawa. A lokacin muna turawa ana karantawa muna jin mutane daga jihohi kamar ni daga jihar Katsina da Zaidu Bala daga jihar Kebbi da Saleh Shehu Ashaka daga Jos da Ali Jauro daga Kano da dai sauransu.
    Daga nan muka fara kokari har Allah ya taimake mu a cikin shekara ta 2008 muka kafa wannan kungiya muka sanya  mata sunan muryar talaka. A shekara ta 2010 ne muka fara yin babban taron wannan kungiya.  Mun yi zaben shugabannin wannan kungiya a shekara ta 2013 a Katsina.
    Manufar wannan kungiya shi ne a yi amfani da kafofin yada labarai kamar gidajen  rediyo da jaridu na cikin gida da waje  a dauki kukan talaka, a fada wa duniya da shugabanni a matakan kananan hukumomi da jihohi da tarayya gabaki daya. Saboda haka an kafa wannan kungiya ne domin ta habaka muradun talaka da kare hakkinsa ta hanyar kafafen yada labarai. Don haka za ka ga dukkan ayyukan wannan kungiya ya ta‘allaka ne ga kafofin yada labarai da jaridu. Kuma muna shirya tarurrukan kara wa juna sani da wayar da kan al’umma.   
    Kuma kamar yadda na yi bayani ayyukan wannan kungiya sun ta’allaka ne kan wayar da kan a’umma da yadda za a sami shugabanci nagari  da yadda za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan. Bayan haka akwai aikace-aikace na jin kai da muke yi misali kamar taimaka wa marayu da kai ziyara gidajen yari don fitar da fursunoni da ziyartar asibitoti don tallafa wa marasa lafiya da dai sauransu. Wadannan su ne kadan daga cikin manufofin kafa wannan kungiya.
     
    GTK: Daga lokacin da kuka kafa wannan kungiya zuwa yanzu kuna da  mambobi guda nawa?
     
    Kwamared Bashir Dauda: Ya zuwa yanzu muna da rassan wannan kungiya a jihohi 16 na arewacin kasar nan. Haka kuma muna da wakilai a kudancin kasar nan da wasu kasahen Turai da Afrika  kamar  jamhuriyar Nijar da Chadi da Sudan da Saudiya da Amerika da Ingila duk muna da wakilai a wadannan kasashe. Kuma a takaice ya zuwa yanzu muna da mambobi sama da mutum dubu 50 a ciki da wajen Nijeriya. 
     
    GTK: Daga lokacin da kuka kafa wannan kungiya zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne kake ganin kun samu?
     
    Kwamared Bashir Dauda: Babbar nasarar da muka samu a wannan kungiya ita ce tun da muka kafa wannan kungiya   har ya zuwa wannan lokaci ba mu taba tsayawa wajen gudanar da ayyukan wannan kungiya ba. Muna rike da wannan kungiya kuma muna gudanar da ayyukanmu. Idan ka dubi yanayin yadda kungiyoyi suke tafiya a Nijeriya, wannan ba karamar nasara ba ce. Domin za ka ga wata kungiyar ma ko shekara daya ba ta yi a raye sai ka ga ta mutu.
    Nasara ta biyu ita ce har ya zuwa yau wannan kungiya tana nan kanta a hade. Saboda shugabannin wannan kungiya suna yin komai bisa gaskiya da rikon amana . Abu na uku yau a Nijeriya da duniya gabaki daya babu inda ba a san sunan wannan kungiya ta muryar talaka ba.
    Wata babbar nasarar kuma da muka samu ita ce, wannan kungiya a kullum tana gwagwarmaya kan yadda talakan Nijeriya zai sami \’yancin kansa. Wannan ya sa shugabanni da yawa suna tafiya da wannan kungiya. A cikin gwagwarmayar da muka  rika yi a Nijeriya, a yau muna da mutane daban-daban da suke cikin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi. Saboda ana tunanin duk dan kungiyar muryar talaka mutum ne mai gaskiya da adalci da rikon amana. A cikin irin mutanenmu da aka zabo aka saka a cikin gwamnatin tarayya akwai ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung. Kowa ya san wannan mutum dan kungiyar muryar talaka ne kuma kowa ya san irin gwagwarmayar da ya yi ta kare hakkin talakawan Nijeriya da kuma ganin an sami hadin kai a tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban na Nijeriya. A takaice yana daya daga cikin mutanen da suka ba da gudunmawa wajen kawo zaman lafiya a Nijeriya. Wannan ne ya sanya shugaban kasa Muhammad Buhari ya dauko shi ya ba shi mukamin minista a cikin wannan gwamnati.
    Bayan haka akwai Bashir Ahmed mai taimaka wa shugaban kasa Muhammad Buhari  kan kafofin yada labarai na zamani shi ma dan wannan kungiya ne.
    Haka idan muka koma ga jihohi  mataimakin gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala shi ma dan wannan kungiya ne. Muna da mutane da dama a cikin gwamnatoci jihohi musamman jihohin arewacin kasar nan. Kuma muna da iyayen wannan kungiya masu hali, wadanda suke taimaka mana a kowanne lokaci. Don an ce muryar talaka ba wai ana nufin talauci ba ne. Ana nufin kungiya ce wadda take daukar bukatun talaka ta kai su inda ya kamata, domin a sami maslaha.
    Kuma mutane da dama suna zuwa su sami wannan kungiya su roki ta yi masu jagora don warware wasu matsaloli. Misali kamar a jihar Zamfara wannan kungiya akwai mutane da yawa da suka sami matsaloli na rashin lafiya kamar yin tiyata a asibiti, mun hada su da mutane sun taimaka masu. Akwai wasu mutane marayu a Sakkwato da aka so a cinye wa gona wannan kungiya ta taimaka wajen daukar lauyoyi muka tabbatar an yi adalci aka maido masu da gonarsu.
    Haka kuma a kwanakin baya wannan kungiya ta shirya taron gangami a jihar Katsina na bayar da magunguna kyauta. Mun shirya gasar karatun Alkura’ani mai girma  a Katsina mun raba wa wadanda suka zama zakaru kyaututtuka a wajen gasar.
    Ga maganar wayar da kan talakawa yau a duniya da wuya ka bude rediyo ba ka ji wani dan wannan kungiya ya ba da gudunmawa kan wata matsala ko wata muhawara wadda za a sami shugabanci nagari a Nijeriya ba. Wadannan su ne kadan daga cikin nasarorin da wannan kungiya ta samu.
     
    GTK: Mene babban burinku?
     
    Kwamared Bashir Dauda: Babban  babban burinmu shi ne talakan Nijeriya ya sami \’yanci kuma Nijeriya ta gyaru.
     
    GTK: A yanzu wadanne abubuwa ne kuka sanya a gaba?
     
    Kwamared Bashir Dauda: Yanzu muna fuskantar babban taro da za mu gudanar a ranar Juma’ar nan a garin Gusau babbban birnin jihar Zamfara. A wurin wannan taro ne za a gabatar da kudiri wanda zai bayar da dama ko a rusa shugabannin wannan kungiya a sake zabe ko kuma a ce su ci gaba. Sannan kuma a wajen wannan taro za a kawo sababbin dokokin wannan kungiya, idan ‘yan kungiyar suka amince shi kenan sun zama doka.
    Bayan an gama wannan taro abu na gaba shi ne maganar gyara fasalin kasar nan. Akwai  rubutu da muka yi kan wannan magana. Muna son mu gabatar wa majalisar kasa da majalisun jihohi  wannan rubutu da muka yi. Wanda muna fatar  zai taimaka wajen kawo gyara ga wannan al’amari.
     
     
     
     
     
     
     
     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here