Karya Rahama Take Yi Ta San An Dakatar Da Ita – Baharu

0
1057

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba.

KUNGIYAR masu shirya fina-finai ta kasa reshen jihar Kano, MOPPAN ta karyata rashin korar da  jarumar shirya fina-finan hausa Rahama Sadau ta ce an yi mata daga MOPPAN . babu wanda ya kore ta  daga kungiyar saboda a tunanin ta ita bata aikata wani laifi ba da zai sa a kore ta daga kungiyar ba.   Jami’in hulda da jama,a na kungiyar Alhaji Balarabe Murtala Baharu, ne ya karyata kalaman nata hirar su da wakilin mu .

Ya ce shekara guda ke nan da zartar da hukuncin korar ta daga kungiyar masu shirya fina-finai ta Kano kuma an bata wa’adin kwanaki 30. ata gurfana gaban kwamitin da kungiyar ta kafa domin ta zo ta kare kanta amma kememe Rahama ta shalle ta ki halarta amma sai ga shi tana fada wa duniya ita ba a kore ta ba .

Kwanan baya ne aka ce Sadau ta yi hira da wata kafar yada labarai amma ba masu wallafa jaridun NewNigerian da Gaskita tafi kwabo ba. Da aka tambaye ta a hirar ta waccan kafar yada labarai game da korar da moppan ta yi mata ita kuma Rahama ta ce ita ba ta san da wannan batu ba .Ana zargin Rahama Sadau dai da wani lokacin can baya ta saba wa dokokin kungiyar ne tsakanin wata mu’amala   tsakaninta da wani mawaki.

Kakakin kungiyar masu shirya fina-finan ta kasa reshen Kano ya ci gaba da cewa \” Abin da na riga na sani ina daga cikin mutanen da suka zauna suka yi wannan hukunci ,kuma ina daga cikin na farko da suka zauna suka tattauna kan wannan hukunci suka fada har a gidan rediyo, ga ma takardar da muka fitar cewar Rahama bisa wasu abubuwa da ta yi ta saba ka’ida da dokokin tafiyar da shirin fim a jihar Kano, babu wani wanda ya ce ko a Kano ,ko a Kaduna ko a Sakkwato, amma a jihar Kano ne aka ce an kore ta daga harkar fim ta Kano kuma wannan abun ya faru kusan shekara guda kenan kuma har yanzu babu wani wanda ya ce ya mayar da ita kuma lokacin da aka yi wannan sanarwa shugaban kungiyarmu reshen jihar Kano Kabiru Maikaba ya fito ya fada kuma ya fadi cewar an kafa kwamiti aka ce idan Rahama tana da korafi ga kwana 30 nan ta zo ta yi bayani gaban wannan kwamiti har ya zuwa yau ba na jin din Rahama ta zo ta gana ko ta yi korafi a rubuce cewar ga shi kaza-kaza-kaza yanzu ga abin da aka yi ga abin da take so a yi\”.injishi.

Alhaji Balarabe Baharu,da wakilinmu ya tambaye shi yana ganin idan ita Rahama ta zo ta nemi a yafe mata gaban wannan kwamiti za a yafe mata domin a wuce wurin sai ya ci gaba da cewa \” mutum ne da dansa ya ce fita ka bar min gidana,amma idan kana da dalili da ka ge ganin za ka dawo ka zauna to ka samu wane ka yi masa bayani sai ka dawo\”.Karshe jami’in hulda da jama’a na kungiyar masu shirya fina-finan hausa ta kasa reshen jihar Kano ya shawarci jarumar da cewa durkusa wa Wada ba gajiyawa ba ce \”babu wanda zai ce Rahama ba tauraruwa ba ce ,babu wanda zai ce Rahama ba ta wakiltar kasa Bahaushiya ce Musulma ce abun da ake magana shi ne mutum ya yi kuskure ya yarda ya yi kuskure, Allah ma ana masa laifi ya yafe mana balle dan uwanka dan Adam,babu wani mutum da zai hana Rahama ci gaba hasali ma tana yin abin da mutane suke yaba mata shi ke taimaka wa al’umma \”ya ilahi idan ka ce Rahama ba za ta yi fim ba sai me za ta yi amma ta yarda ta yi kuskure\”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here