Jami’an Kwastan Sun Kama Kwantenar Macizai Da Aka Shigo Da Su Daga Kasar Kamaru

0
952

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

JAMI’AN kwastan a Kalaba Jihar Kuros Riba sun kama kwantena uku zokare da buhunan macizai da sauran kwari buhu 140 da aka shigo da su Nijeriya ta ruwa daga kasar Kamaru.

Sauran kwarin da Gaskiyatafi kwabo ,  ta samu labarin an shigo dasu ta ruwa sun hada da shanshani, samfurin burduddigi, gizo-gizo da aka shigo dasu kasar nan domin sayar wa ,kiwo da kuma sauran bukatu an kiyasta kudin su zai kama kimanin naira milyan shida da rabi.

Da yake yiwa manema labarai karin bayani game da kamen da sukayi a gavar ruwan kalaba kwamandan shiyar jami,an kwastan mai kula da kuros riba, da Akwa Ibom  Misis Nanbyen Burromyyat, ta ce jami,anta ne da ke aikin sintiri suka kama kayan.Ta kara da cewa kayan da aka kama sun saba doka sashe na 3 data haramta safara da kuma fataucin irin wadan nan halittu.

Kwatirolar taci gaba da cewa saboda tsoron kada halittun a bude su domin a gani su fito wasu su tsere ne yasanya ta kin amincewa da a yi hakan amma fa ta ce ta mika masu laifin da ake zargi da kayan su ga hukumarukan gona da kuma  kebe halittu da kwari domin su  tantance kwarin   kuma  suci gaba da bincike a kan su .Hukumar har wayau tace tun 24 ga watan Yuli ne aka shigo da kayan hukumar su ta yi sa,ar kamawa.

Babbar jami,ar kwastan din har wa yau da aka tambayeta ko me take ji za,ayi da wadan can  dasu Allah ya huwacewa kasar nan nau,in macizai da ba  sai wani yaje wata kasa ya shigo dasu ba .Daya daga cikin masu kayan da ya  shigo da kayan daga jamhuriyar kamaru mai suna Julius Yoyigana ya shaidawa wakilinmu  cewa shi bai san abinda buhu nan suka kunsa ba shidai “abokina ne ya bani yace ga sako nan in kaiwa wani amininsa a legas abinda nake dashi lambar wayar wanda zai karbi kaya da na buga masa waya sai yace in jira shi anan kalaba akwai wani wanda zai zo ya karbi kayan a hannuna.injishi

Shi kuwa direban jirgin, Victor Agbor, ya gayawa ,yan jarida cewa basu kula dakunshin kayan ba a cikin jirgin kafin su taso daga kamaru zuwa nan nijeriya sai da  muka zo nan nijeriya ne aka sanar dani cewa akwai kayan a cikin jirgi na.inji Agbor direban jirgin ruwan da ya  kawo buhunan macizai nijeriya, daga kamaru.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here