Fim Din Mutuncin Mace Na Dauke Da Darussa Da Damar Gaske

0
1298

MUSA MUHAMMAD KUTAMA  Daga  Kalaba

AHMAD MUHAMMAD  matashi ne da tauraruwarsa ke yin haskawa  a masana,antar  fina-finan hausa ta  Kannywood ,kuma shugaban kamfanin shirya fina-finai na BIG TIME   jarumin ya taka mahimmiyar rawa a duk fina-finansa da ya yi  kuma suka shahara kamar fim din mata da maza. Jarumin yayi fice  a takarawar yin soyayya da matan aure a roll din  fim da duk ya fito shine ma wanda ya fito a roll din wanda ya  sace jakar  kudi cike da kudi Dalar Amurka ba,a sani ba a gidan Ali Nuhu .

Ga mace ga  miji  fim ne da jarumin ya fito wanda yake nuna illar matsalar da ke afkuwa halin yanzu tsakanin ma’aurata da kafin a yi aure saboda tsabar son juna da suke yi kamar kowa ya hadiye kowa amma abin mamaki sai kaga abubuwa na canjawa  wasu matan kuma da zarar sun samu mazan su sun bar su sun shiga jami’a ko kwaleji sai su  jingine tabarmar auren su su mayar da kan su zawarawa ko ‘yan mata suyi ta soyayya da samari Haka nan kuma fim din yana nuna illar macen aure da idan ta samu shiga babbar koleji ko jami,a karatu take ajiye rigar aure ta tubeta sai kaga sun saje da ,yan mata da zawarawa suna ta sheke ayarsu.

Sauran fina-finan da jarumin ya fito masu zuwa sun hada daga mace ga namiji, da sama da kasa yadda da kuma mutuncin mace. Ga yadda tattaunawar su ta kasance:-

GTK: Gabatar mana da kanka ?

Ahmed Muhammad:  Sunana Ahmed Muhammad mai kamfanin shirya fina-finan hausa na BIG TIME dake Kano.

GTK: Harkar fina-finan hausa wasu sha,awa ce ta kawo su cikinta yayinda wasu kuma dama suna da burin yenta ian sun samu hali kai me ya ja hankalin ka ka shiga harkar fina-finan hausa?

Ahmed Muhammad: To ni gaskiya Alhamdulillahi ni ba  sha’aw a ce ta kawo ni ba  ba kuma wani ne ya kawo ni ba dama can ina da ra’ayi dama can ni, ni na kai kaina .

GTK: Ta wane mataki ka fara fim tunda ka ce ba karkashin wani ka fara ba ba kuma wani ya jawo ka ba?

Ahmed Muhammad: Ai abin da yawa gaskiya ba ina shigowa na fara fina-finai ba sai da da zan yi wasu ayyuka haka tukuna da wasu mutane daga baya sai nag anima ai yakamat in shigo domin in bayar da taw a gudunmawar tunda kaga kowa yana da irin nasa tunanin  na daban to shi ne nake ganin ni ma in bayar da nawa tunanin inda nake ganin ya fi dacewa shi ne na fara shirya wannan fina-finai .

GTK:kafin ma ka fara shirya fim naka na kanka ai ka yi wasu hala ,ko za ka iya fada mana nawa ka yi da kuma sunayen wasu  ?

Ahmed Muhammad: EEh! Gaskiya bazan iya tuna adadin fina-finan da nayi ba don gaskiya suna da yawa kuma na taka rawa iri-iri amma akwai wadan su na fi taka rawa mahimmiya a cikin su.

GTK:kamar wane da wane?

Ahmed Muhammad:kamar roll da naïf takawa a fim shine kamar inayin soyayya [dariya] mh! Murmushi  kama soyayya da matan aure a fim.

GTK: Wannan rawa da ka ce kana takawa a fim ko ka taba fuskantar wani kalubale ko tsangwama daga masu kallon fina-finan ku ganin cewa kana soya da matan aure a fim na taba hira da wani jarumi da yayi fim din Wasila ya taba fada min a hira da na yi da shi cewa akwai wani tsoho da shiga mota ta hada shi da shi a tashar mota ya rika zaginsa kai hatta ma ‘ya’yansa a makaranta sun rika shan tasku hannun dalibai ,yan uwan su saboda rawar da jarumin ya taka a fim din wasila ko ka taba fuskantar makamancin haka?

Ahmed Muhammad:Eh! To gaskiya Alhamdulillahi a gaskiya ni dai ban taba fuskantar kalubale irin wannan ba sai dai dan abin da ba a rasa ba sai dai wani abu dana fuskanta da zan iya kiransa kalubale kamar irin haka mata da muke karatu dasu a makaranta ban san wasu ba amma nasan suna tsokanata na san cewa tsokana ce kurum suke yi min wasu ko da gaske suka yi ko ba da  gaske ba su dai suka sani gaskiya sai kuma Allah da ya yi su amman abin da na san na tava fuskanta .

GTK: Kai ne Shehu miji a fim din maza da mata roll da ka fito a fim din shine sace jakar da maigida yazo da ita wadda a ke zato kudi Dalar Amurka ce a ciki lamarin da ya jefa matar gida cikin matsala tsakaninta da mijinta mene ne hikmar hakan domin masu karatu za su so sanin hakan?

Ahmed Muhammad: To ! gaskiya ne ni ne na fito a cikin wannan fim din na maza da mata a sunana  Shehu miji  a fim din duk rigimar fim din ma idan ka duba ai a kaina ake yinta ita Rahama ta kasance matar aure matarsa ni kuma mun hadu a makaranta irin kawai muka fara soyayya da ita har ma ta nemi in rika koya mata karatu  muna dai dan yin haka muna badda  bami to mun yi da ita zan zo gidan in kwana domin in koya mata karatu ina zuwa gidan da na yi sallama naji ba,a amsa ba alamun bata nan tun da daman a saba zuwa gidan ni kuma naga jaka a falon ta da  daloli a ciki kawai na yi awon gaba da ita na yi tafiyata na yi nawa waje .

Ita ma ba ta san na kauka ba sai daga karshe ta sha wahala ni ma na sha wahala a kotu .

GTK: Ban da wadannan fina finan akwa wasu da kake yin aiki a kan su yanzu ?

Ahmed Muhammad: Eh! Akwai wasu fina-finai  guda 3. Akwai  ga mace ga namiji, da akwai mutuncin mace, akwai sama ta kasa.

GTK: Mai karatun mu zai so sanin ma’anar fim din mutuncin mace wane darasi zai koyar?

Ahmed Muhammad: To Alhamdulillahi wannan labari  gaskiya zai koyar da darussa iri-iri kadan daga cikin su shi ne  al’umma ta gurbace da yawan tallace-tallace,za ka ga mace iyayen ko suna da hali ko ba su da shi  ya kamata   a ce ta yi karatu ,karatun kuma kowane iri ne domin shi zai taimaka mata shi zai bata dammar tarbiyyar tar da dukannin al,ummar da Allah ya hada ta da su  nan gaba ba sai lallai ‘ya’yanta ba tun da dama tarbiyya a hannun mata take .

Wannan fim mutuncin ‘ya mace labari ne da yake magana akan ainihin rayuwar mata da ko yaya da kuma ko a yaya suka tsinci kan su ya fi kyau a ce suna da ilmi, su rika zuwa makaranta wannan ilmi shi ne zai rika taimakawa rayuwar su dama sauran mutanen da take tare da su.A takaice wannan shi ne dan takaitaccen bayani a kan fim din mutuncin ‘ya mace.

GTK: ga wanda duk ya karanta wannan tattaunaw ada mukayi a wannan jarida wane roll kafi fitowa a fim domin makarantan mu su gane kai ne?

Ahmed Muhammad:  A fim naïf fitowa a roll na soyayya,soyayya da matar aure gaskiya .

GTK: a fina-finan da kake shiryaw akana fitowa cikin su kokuwa sai dai kasanya wasu su fito?

Ahmed Muhammad: A,a gaskiya bana fitowa a ciki .

GTK:  Wasu jama’a  na yi wa ‘yan fim zargin masu bata tarbiyya ne wasu kuma suna ganin cewa ba haka abin yake baya ka rika kallon wancan zargi kafin ka shigo a kuma ka tsunduma cikin harkar ko ka ga hakan?

Ahmed Muhammad: To ka san kowa da irin tasa fahimta  an ce fahimta fuska na san a gaskiya ba akwai irin wadannan maganganun amma ni gaskiya ba fuskanci irin wannan  kalubalen ba da yawancin mutane mu suke fuskanta ba tunda ni gaskiya ba boyayye ba ne ba na yi karatu don ban ma fara harkar fim ba sai da na sauke alkur’ani ,sannan kuma karatun boko har yanzu ina yinsa mafiya yawancin mutane masu kallona a fim sun riga sun san ko waye ni  sun san abin da zan yi sun san wanda ba zan yi ba to gaskiya ban fuskanci wannan kalubalen ba .

GTK: Ga shi kun zo Kuros Riba aikin ku yayin da wasu kuma ke kuyar zuwa ya kuka samu al,umma musamman ‘yan arewa mazauna Kurmi ?

Ahmed Muhammad: Gaskiya ba mu  fuskanci wata barazana ba  da muka zo nan Kalaba  mun ga yadda ma irin yadda  ‘yan uwanmu  ‘yan arewa mazauna Kalaba suka karbe mu hannu bibbiyu mun gode Allah bar zumunci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here