EFCC Ta Cafke Wani Mutum Da Katin ATM 849

0
762
Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna

WANI mutum mai suna Yasir Salisu Abdullahi, ya shiga hannun jami\’an hukumar EFCC biyo bayan kama shi da katunan cire kudi har dari takwas da arba\’in da tara.
An dai kama Yasir Salisu Abdullahi ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu da ke birnin Kano.
An kama shi ne biyo bayan duba kayansa da aka yi kamar yadda dokar binciken kaya ta tanadar.
Shi dai wannan mutum ya yi kokarin fita ne daga Nijeriya ta filin jirgin.
Su dai hukumomin sun yi bayanin cewa za a ci gaba da gudanar da binciken inda ya samo wadannan katuna da inda za shi da su da kuma abin da zai yi da wadannan katuna masu yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here