Gwamnatin Yobe Ta Wuce Tsara Kan Batun Ilimi

0
1017
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
KWAMISHINAN ilimin jihar Yobe, Alhaji Mohammed Lamin ya bayyana cewa
gwamnatin Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ta jihar Yobe gwamnati ce da ta
kafa tarihi wajen wuce tsara dangane da bunkasa harkokin ilimi
musamman ta hanyar ginawa, da gyara manya da kananan makarantun jihar
tare da kayan aikin koyarwa.
Ya kara da cewa gwamnatin ta dauki ingantattun matakai wajen kyautata
yanayin jin dadin malamai a kowanne mataki wajen biyan albashi bisa
kan kari kana da biyan hakkokin wadanda lokacin ritayar su yayi.
 Muhammad Lamin ya ci gaba da cewa \”jihar Yobe tana daya daga cikin
jihohin yankin arewa maso-gabas wadanda rikicin Boko-Haram ya yi wa
mummunan lahani, inda baya ga salwantar dubun-dubatar rayukan al\’ummar
jihar ciki har da daliban jihar. Wannan ya jawo koma baya matuka gaya a bangaren
ilimi bisa ga yadda maharan suka ringa kai munanan hare-hare a makarantu tare da
jawo hasarar rayukan daliban jihar. Kuma wannan waki\’a ta shafi kusan
kowanne yankin jihar. Gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin
sauke nauyin da ya hau kan ta tare da zage dantse inda ta sake gina
makarantun firamare sama da 24 da gina ajujuwa sama da 400. A dare
guda kuma da samar da isassun kayan koyarwa tare da katange mafi yawan su domin
inganta tsaron makarantun\”.
\”Har ila yau kuma, makarantun da suke a yankunan kananan hukumomin Gujba,
Gulani, Damaturu, Tarmuwa, Yunusari da Geidam, su ne suka fi dandana kudar
wannan bahallatsar konawa da rusawa baki daya duk da makarantu da ke
yankin Gujba da Gulani kuma sun fi sauran, saboda nasu ruguzawa ne
baki daya zuwa toka. Amma duk da hakan, gwamnatin jihar Yobe ta sake gina su zuwa
sabbi fil bayan kwaskwarimar wasu makarantun sakandaren garuruwan
Yunusari, Gwio-kura da makamantansu \”.
Bugu da kari kuma ya ce, a wancan lokacin, alkaluman da muke da su sun
nuna cewar a Gujba da Gulani, baki daya \’yan ta\’addan sun ragargaza
su zuwa kufai. Dangane da hakan, sake gina wadannan makarantun da Boko
Haram suka rusa ya fi karfin gwamnatin jihar Yobe ita kadai, bisa ga haka kuma ta
nemi tallafin gwamnatin tarayya da kungiyoyin ba da agaji tare da
daidaikun masu
ba da jin kai domin sake farfado da ilimin jihar. Duk da wannan,
gwamnatin Yobe ba ta karaya ba, a haka ta tunkari matsalar kuma ta ci
galabarta cikin nasara.
Alhaji Muhammad Lamin ya kara da cewa,  muhimmin matakin da  gwamnatin
ta dauka domin kara daga martabar ilimin jihar shi ne daukar daruruwan
kwararrun malamai domin maye-gurabun da ake da su a fannin. Yayin da a
kwanan baya Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ya ba da umurnin daukar kwararru da suka samu horo a fannin koyarwa, masu shaidar karatun Digiri, NCE da HND a makarantun
jihar domin yi wa anniyarsa kan-da-garki dangane da bunkasa ilimi a jihar. Sabbin
daukar wadanda aka kai su a fannin  kimiyya da fasahar jìhar wato Science and Technical Schools Board (STSB), Teaching Service Board (TSB)\”.
Alal hakika wannan yunkuri na bai daya tare da kafa dokar ta-baci da
gwamnatin jihar Yobe ta yi a sha\’anin ilimin kanana da matsakaita da manya, ma\’aikatar
ilimin jihar Yobe ta samar da isassu kuma ingantattun kayan bukata. Zancen
da ake ciki yanzu aiki ya yi nisa dangane da sake gina tsoffin makarantun
tare da wadanda suka tagayyara da kawata su da samar da kwararrun
malamai- wannan abin ban sha\’awa da burgewa ne kuma hangen nesa da yi wa hancin ci gaban jihar tubka mai ma\’ana. Matakin da ya dawo da al\’ummar jihar cikin
hayyaci bayan kusan yanke tsammani.
Ta bangaren manyan makarantu mallakin jihar kuwa, wadanda suka kunshi
Jami\’ar jihar Yobe, Umar Suleiman College of Education, Gashuwa da Mai
Idrissa Alooma Polytechnic, Gaidam, CABS Potiskum, College of Legal
Studies, Nguru, College of Nursing Damaturu da College of Agriculture,
Gujba da makamantan su. Alhaji Muhammad Lamin ya nuna cewar babu mai tababar yadda gwamnatin jihar ta sake bunkasa su tare da dora su bisa kan sahihiyar
alkibla. A cikin \’yan kwanakin nan ne hukuma mai kula kwalejojin ilimi ta Nijeriya NCCE ta bayyana cewar kwalejin ilimin jihar Yobe(Umar Suleiman College of
Education, Gashu\’a) ta tsere wa takwarorin ta dake yankin arewa maso-gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here