MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba.
KUNGIYAR dillalan man fetur ta masu zaman kan su kasa IPMAN reshen jihar Kuros Riba ta koka kan irin yadda wasu kamfanonin da ke sayar musu da albarkatun man fetur ke nuna halin rashin dattaku.Alhaji Isah Umar daya daga cikin ‘yan kasuwar da ya sayi kaya kakar farashi amma daga bisani saboda kayan farashinsa ya karu kamfanin da ya saya ya nemi tilasta masa sai ya dora kudin da suka karu bayan ya sayi kayan kafin ya dauka.
Alhaji Umar wanda ya yi tir da halayen kamfanin sayar da mai na Samson dangane da karin kudin da ya yi masa ya sanya tilas ya biya. A zantawarsa da wakilinmu ya ce “abin mamaki na sayi man fetur kan farashi amma da yake kafin in dauki kayan an samu karin naira biyu a kai sai kamfanin ya ce ba zai ba ni mai ba har sai na dora wannan karin naira biyu da aka samu a kai kafin a ba ni kaya”.Lamarin da dan kasuwar ya tubure ba zai kara ko kwandala ba a kai .
Ya ci gaba da cewa daga nan har matatar mai ta Warri idan aka sayi kaya in dai kafin mutum ya dauka aka samu karin farashi koda na sisin kwabo ne sai su ce sai mai kaya ya biya kafin a ba shi wanda hakan “ba adalci ba ne “inji shi.
Wannan jani-in jaka da ke faruwa tsakanin Alhaji Isah Umar da kamfanin Samson masu daffon ajiye man fetur suna sayarwa da lasisin gwamnati ya tababtar da cewa matukar ‘yan kasuwa masu hali irin na wancan kamfani ba su sauya tunanin su ba suka rika kamanta gaskiya, to nan gaba fa ba za su kai labari ba.
Da wakilinmu ya tuntubi mista Ugochukwu mataimakin manajan sayar da mai na kamfanin domin jin ta bakinsa game da lamarin ya zuke ya ce “ni ba ni da ikon yin magana da ‘yan jarida amma kayan su da suka saya za a ba su”.sai ya kashe wayarsa .Kamfanin mai na north west masu hada-hadar man fetur ne kadai suka ciri tuta a wajen kamanta gaskiya a harkokin su na kasuwa kamar yadda Alhaji Isah Umar ya tabbatar wa manema labarai da suka garzaya kamfanin domin jin yadda lamarin tsakaninsu yake gudana.