GWAMNATIN YOBE TA SAMAR WA MATASA KIMANIN DUBU 20 DA MATAN DA BA SU DA GALIHU AIKIN YI.

0
700
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
A kokarinta na kawar da zaman banza a tsakanin al\’ummarta musamman
matasan da suka kammala makarantun gaba da sakandare kafin su samu
kwakkwarar madafa, gwamnatin Jihar Yobe ta ce a yanzu haka ta samar wa
matasa kimanin dubu 20 aikin yi na wucin gadi da ake ba su alawus na
Naira dubu 15 a duk wata.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim
Gaidam a jawabinsa ga al\’ummar jahar dangane da irin kokarin da
gwamnatinsa ke yi wajen samar wa da matasan jihar aikin don rage zaman
kashe wando.
Gwamnan ya kara da cewar cikin matasa dubu 20 da suka kammala
karatunsu da ke cikin wannan shiri kimani matasa 5,500 daga cikinsu
nada takardun shaidar kammala Digiri ne da Babbar diploma  ta kasa HND
da takardar malunta mai daraja ta daya NCE sai kuma matasa 6,572 da ke
da takardar karamar diploma ta kasa OND.
Ya kara da cewar dukkannin matasan ana basu alawus din ne da manufar
cewar matukar ka samar wa matasa aikin yi  da za su daina zaman banza
to kuwa ka rage wa jaha da kasa baki daya wani babban bangare da zai
taimaka wajen samar da zaman lafiya domin rashin aikin yi shine kan
gaba wajen samar da barazanar tabarbarewar harkokin tsaro a
tsakankanin al\’umma.
Gwamnan ya kara da cewar baya ga samar wa matasan aikin yi har ila yau
kuma gwamnati tunin ta ware matan da basu da galihu wadanda aksari sun
rasa mazajensu  a sanadiyar rikicin Boko da Jihar ta yi fama da shi a
baya yadda hakan ta sa  yankin an barsu da
yara marayu an basu dubu 10 kowaccensu don su yi jari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here