Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
WANI hanshakin dan kasuwa Alhaji Gambo mai citta da ke babbar kasuwar
Potiskum a Jihar Yobe ya bayyana cewar, yaki da cin hanci da rashawa
da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi don kai kasar nan ga
tudun tsira tunin an kai ga nasarar wannan fafutuka.
Alhaji Gambo mai citta ya bayyana hakan ne a tattaunawarsu da GTK a
garin Potiskum dangane da ce-ce-ku-cen da wasu ke yi na babu abin da
wannan gwamnati ke tabukawa.
Ya kara da cewar, wannan yaki da cin hanci da rashawa da shugaba
Buhari ya dukufa don yi ai ba ga kowa ya taimaka ba illa ga mu \’yan
kasa.
Shi ya sa ma akullum muke masa addu\’ar Allah (SWT) Ya taimake shi bisa
ga wannan kudiri nasa wadanda kuma suke masa zagon kasa kan wannan
tsarkakakken aiki nasa na yaki da almundahana to su saurari
sakamakonsu
daga Allah (SWT) domin ba masu kaunar kasar nan bane.
Ya kamata al\’ummar kasa su sani cewar, wannan aiki da gwamnatin
Muhammadu Buhari ke yi ta na yi ne ba wai don amfanin yanzu kawai bane
aiki ne da zai amfani kasa har illa masha Allahu matukar an kai ga kakkabe dukannin
bara-gurbi domin ai yanayi ne don ceto tattalin arzikin kasa da kuma al\’ummarta.
Kuma ma ai ayyukan da Muhammadu Buhari ke yi kan abin da ya shafi yaki
da almundahana ayyuka ne da ya kyautu dukannin \’yan kasa mu tsaya mu
yi masa godiya tare da addu\’ar Allah madaukakin Sarki ya kara kare shi tare da
bashi karfin gwiwar ci gaba da sauke nauyin al\’ummar da ya dauka.