Sama Da Naira Biliyan 30 Muke Sa Ran Za Ta Iya Gyara Barnar Da \’Yan Boko-Haram Suka Yi A Yobe

0
686
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GWAMNATIN Jihar Yobe ta bayyana cewar, adadin kudaden da gwamnatin
jihar ke bukata don gyara irin barnar da rikicin \’ya\’yan kungiyar
Boko-Haram ya haifar wa gwamnati da daidaikun al\’umma da ya shafi
gine-gine da makamantansu zai kai kimanin akalla Naira Biliyan 30.2
don mayar da komai ya koma kamar yadda yake a baya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim
Gaidam wanda mataimakinsa Injiniya Abubakar Ali ya wakilta a yayin
bikin rarraba kayayyakin tallafin da wata hukumar da ke bada tallafi
ga \’yan gudin hijjira ta gwamnatin tarayya a karkashin wani kwamiti da
shugaban dakarun rundunar sojan sama na kasar nan Air Marshal Sadik
Abubakar  ga \’yan gudin hijirar  da suka koma garinsu na Buni Yadi da
ke karamar hukumar Gujba a kwanakin baya.
Gwamnan ya kara da cewar, matukar suka samu wadannan makudan kudade
labudda za su taimaka matuka ta wajen mayar da gurbin mafiya yawa daga
cikin barnar da rikicin na Boko Haram ya haifar daga bangaren gwamnati
da kuma al\’ummar yankunan da rikicin ya fi shafa.
Da yake jawabi shugaban wannan kwamiti da ya kawo kayayyakin tallafin
daga gwamnatin tarayya shugaban mayakan saman kasar nan Air Marshal
Sadik Abubakar wadda kwamandan runduna ta 79 ta mayakan sama da ke
garin Maiduguri Air Kwamanda Paul N. Dimfiwin ya wakilta ya ce wannan
tallafi na daga cikin yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi  na bada
taimako ga \’yan gudin hijjirar Garin Buni Yadi.
Ya kara da cewar, gwamnatin tarayya na da kudirin talmakawa al\’ummomin
yankunan da suka yi fama da wannan rikici na \’ya\’yan kungiyar Boko
Haram don su samu koma wa ga garuruwansu don ci gaba da gudanar
harkokinsu na yau da kullum kamar yadda yake a baya.
Daga nan sai ya nemi al\’umma da su ci gaba da hada hannu da jami\’an
tsaro don ganin zaman lafiya mai daurewa ya ci gaba da wanzuwa ta
yadda harkokin  rayuwar yau da kullum da suka hada da kasuwanci, ilimi
da makamantansu sun dawo daram dakam kamar yadda suke tun farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here