Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAR hukumar yaki da safarar bil\’adam ta kasa Misis Jolia Okoh ta Nijeriya ta ce ana sa ran cewa yau ne Alhamis za a dawo da \’yan Nijeriya sama da 500 daga kasar Libya.
Ta kuma ci gaba da cewa ya zuwa yanzu an dawo da mutane akalla sama da dubu biyu Nijeriya daga kasashen duniya daban-daban.
Ta ce hukumarta za ta ci gaba da kokarin aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyansu domin kara inganta kyakkawan sunan Nijeriya a idanun duniya.