\’YAN SANDA SUN KAMA WASU SHAHARARRUN YAN FASHI A BINUWE

0
827
Daga Usman Nasidi
HUKUMAR ‘yan sandan jihar Binuwe ta kama wasu shahararren \’yan bindiga wanda ake zargi da sace mutane, Monday Yusufu, wanda aka sani da sunan \’Mad Dog\’ da kuma yaran gidansa a jihar.
‘Yan bindigar sun shiga hannu jamoi’an ‘yan sanda yayin da suke ƙoƙari su kwashe wayoyin mutane a Logo I a garin Makurdi, babban birnin Jihar Benue.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, PRO Moses Yamu a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, ya fada wa jaridar DAILY POST cewa jami’an SARS wadanda suka kama su sun gano wasu manya manya makamai daga gare su.
Yamu ya ce: \”Mun sami wata kira da cewa wasu masu aikata laifuka suna kwace wa mutane wayoyinsu a Logo I a wani yankin Makurdi”.
Majiyarmu ta tabbatar da cewar, Jami\’an SARS masu sintiri sun amsa kiran nan da nan inda suka kama wani dan bindigar Emmanuel Ifeanyi mai shekaru 23, wanda ke cikin kungiyar siri na Red Cross.
Bayan haka, Ifeanyi ya jagoranci jami’an tsaron zuwa ga sauran abokanin aikinsa, Monday Joseph shekaru 26 mai suna \”Mad Dog\” wanda ya yi furci cewa ya yi kisan kai da fashi da dama a Makurdi.
Ƙarin binciken ta haifar da kama Chimezie Ekeke 28, Sonter Joshua, 15, da Hashimu Abdullahi, 27, dukan su maza ne.
“Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike akansu,” in ji Yamu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here