Muhammad SANI Chinade, DAGA DAMATURU
SHUGABAN kungiyar masu sayar da man girki da dangoginsa a Jihar Yobe
Alhaji Umaru Daya mai manja ya bayyana cewar,ya yi matukar na\’amta
dangane da kudirin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ga yaki da tasa gaba da masu handama da babakere da dukiyar kasa.
Ya kara da cewar a matsayinsu na \’yan kasa dama can su sun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da zimmar kwato musu dukiyarsu da wasu \’yan tsirarun mutane marasa kishin kasa suka yi ruf da ciki a kai kamar yadda ya alkawarta musu a yayin yakin neman zabensa, don haka Muhammadu Buhari ya nuna musu halicci da bai jefar da wannan alkawari da ya dauka musu ba, kuma dama mu mun san a rina domin mutum ne mai fada da cikawa.
Kuma wannan irin aiki da ya ke yi muna da yakinin cewar Allah (SWT) zai taimake shi a kan hakan don ganin ya cimma burinsa na kakkabe hannuwan \’yan wawa daga ta\’ammali da tattalin arzikin kasar nan.
Ya kamata a sani cewar duk wadanda ke masa suka bisa wannan kudiri nasa na yaki da masu washe dukiyar al\’umma to fa Allah (SWT) ba zai bar su ba don zai kawo karshensu, kuma mu al\’ummar kasa muna tare da shi dari bisa dari kan wannan kudiri nasa.
\’\’Alal hakika wannan yaki da wannan gwamnati ta shugaba Buhari ke yi da masu zagon kasa ga dukiyar al\’umma wato cin hanci da rashawa ai ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba ma\’ana, ko a yanzu an kai ga cimma nasara domin an yi walkiya na boye ya fito sarari, hukumar da ke yaki da almundahana da dukiyar kasa (EFCC) ta cafke da yawa-yawansu wato masu ruf da ciki da dukiyar al\’umma\’\’.
Don haka akwai bukatar da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari da wannan hukuma ta EFCC da su ci gaba da irin wannan aiki ba tare da gajiya ba wajen kwato mana dukiyar mu da wasu tsirarun mutane marasa kishin kasa suka wawure a matsayin nasu ba kunya ba tsoron Allah tare da kamo su duk yadda suka shiga a doron kasa don hukunta su ya zama ishara ga \’yan baya.