Ba Mu Da Masana\’antar Rake Sai Hakori – Nuhu Kidandan

0
1061
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

AN bayyana arewacin Nijeriya da cewa shi ne koma baya a daukacin yankunan kasar da ke noman rake amma babu wata masana\’antar sarrafa shi sai hakori.
Tsananin koma baya ne duk ya jawo mana irin wannan rashin ci gaban da ya yi mana kanta a cikin al\’umma.
An bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan rediyon tarayya na Kaduna wanda Hakimin kasar Kidandan Alhaji Lawal Nuhu Umar, ya fayyace cewa duk yankin arewacin kasar babu kamfanin sarrafa rake sai hakori kawai.
Lawal Nuhu Umar, ya ci gaba da cewa a zahiri masu sayen masara da sauran amfanin gona suke da kamfanin sarrafa shi don haka sai an tashi tsaye domin samun darajar manoma da abubuwan da suke nomawa.
\”Kashi 60 na noman da ake yi, kananan manoma ne ke yinsa wanda alkalumma suka nuna cewa suna wakiltar kashi 80 na abincin kasar, ta yaya za a yi mu zama kurar baya\”.
Masu kiwon kaji a wani yankin kasar nan suke da kamfanoni da kuma sayen amfanin gonar da yankin Arewa ke samarwa.
Kananan manoma ke ciyar da kasa wanda suka kasance kashi 60 sai manoma na tsaka- tsaka kashi 15 sai manyan manoma da suka kasance kashi biyar kawai a cikin jama ar kasa.
Sai dai jama\’a sun bayyana irin halin da suke ciki a kan batun takin zamani da yake haifar wa yankin matsalar noma
Ina masu kudin arewacin Nijeriya? Da ga \’yan kudu suna kokarin danne manoma amma kowa ya ja bakinsa ya yi shiru
\”Ana bukatar samun metrik tan Miliyan ashirin na masara amma a yanzu ana samun metrik tan Miliyan 7 ne kawai na masara kuma duk daga arewacin kasar ake samunsa, don haka akwai bukatar a ci gaba da samar da wasu shirye-shirye don ciyar da noma da masu yinsa gaba\”. Inji Lawal Nuhu Umar Hakimin Kidandan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here