JAHAR YOBE CE KE KAN GABA DA MASU DAUKE DA CUTAR KODA, AMMA KUMA ZA TA IYA ZAMA TARIHI..Inji

    0
    1050
    Muhammad  Muhammad, DAGA DAMATURU
    CUTAR koda cuta ce dake da matukar hatsari ga Bil-Adama, kuma a zancen
    da ake yi a yanzu wannan cuta ta koda rahotannin masana na nuna kan
    cewar Jihar Yobe ce ke kan gaba a dukan fadin tarayyar kasar nan da ke
    da yawan jama\’ar da ke dauke da wannan cuta ta koda, a kan hakan ne
    GTK ta samu tattaunawa da Kwamishinan ma\’aikatar lafiya a Jahar Yobe Dokta Muhammad Bello Kawuwa inda ya gaskata wannan rohoton da masana da ke cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC)  da ke garin Nguru a jihar suka bayar a kwanakin baya kan cewar, Jihar Yobe ce ke kan gaba a dukan fadin  kasar nan da yawan
    mutane da ke dauke da cutar koda (kidney) tare da kawo irin matakan da
    suke shirin dauka don magance ta.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    Tambaya :- Yallabai, me za ka ce dangane da wani rahoto da wasu masana
    kan harkokin kiwom lafiya cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya
    (FMC) da ke Nguru suka bayar kan cewar, jihar ne ke kan gaba a yawan
    mutanen da ke dauke da cutar koda (kidney) a dukan kasar nan?
    Dokta:- Alal hakika wannan rahoto da ya fito daga masana a asibitin
    Nguru dangane da wannan cuta ta koda tabbas haka ne domin a
    halin da ake ciki  wannan cuta ta koda cuta ce dake shirin zama
    alakakai ga al\’umma kasanc ewar a kullum bazuwa take yi kamar wutar
    daji ta inda ake samun yawaitar masu kamuwa da ita.
    Tambaya:- Wadanne bangarorin jihar ne ake samun yawaitar masu dauke da
    wannan cuta ta koda?
    Dokta .:- Bangaren jihar da aka fi samun yawaitar masu kamuwa da wannan
    cuta dai shi ne  bangaren arewacin Jihar ta Yobe wanda shi ne aka
    fi samun yawaitar masu kamuwa da wannan cuta ta koda babu kakkautawa
    musamman  ma  a kananan hukumomin Geidam, Bade, Jakusko, Yusufari,
    Karasuwa, Nguru da Machina.
    Tambaya:- Daga lokacin da kuka samun wannan rahoto ya zuwa yanzu ko
    akwai wani hobbasa da kuka yi dangane da hakan?
    Dokta ;- A hakikannin gaskiya tun ma kafin wannan rahoto gwamnatin
    Jihar Yobe ta farga ce war, lalle wannan matsala ta cutar koda ta kunno
    kai a jihar sai aka fara daukar mataki, to amma kuma fitowar wannan
    rahoto na masana mai nuna Jihar Yobe ne ke kan gaba a
    masu dauke da  wannan cuta sai hakan ya sa muka shiga bincike ba dare
    ba rana don gano masu dauke da wannan cuta don kai musu daukin gaggawa
    ganin cewar jinya ce da ke da tsadar dawainiyarta da kuma hanyoyin da
    za a bi don shawo kanta to alhamdulillah.
    Tambaya:- Kamar yaya?
    Dokta:- Domin a halin da ake ciki gwamnatin jihar ta yunkura ta wajen
    gano masu dauke da wannan cuta tun tunin tare da daukar dawainiyar
    wasu daga cikinsu da cutar tafi tsamari  inda ake kai su kasashen
    ketare don yi musu magani yayin da wadanda kuma cutar bata yi tsamari
    ba ake daukar dawainiyar wanke musu odar da yi musu magani a cibiyar
    kiwon lafiya FMC da ke Nguru ko wasu asibitocin dabam.
    Bayan haka kuma Gwamna Alhaji Ibrahim Geidam ya ba da umarnin
    kafa kwakkwaran kwamitin masana kan harkokin kiwon lafiya da zai fara
    aiki a sabuwar shekara mai kamawa ta 2016 In Allah ya so don gano
    abubuwan da ke haifar da yawaitar kamuwa da wannan cuta da kuma
    binciken irin ruwan da suke sha da gwada kasar yankunan da abin ya fi
    kamari da sauran dabaru don taka wa lamarin birki.
    Ya kara da cewar dama babban abin da ya ke damunsu shi ne rashin sanin
    mene ne babban abin da ke kawo wannan ciwo na koda a arewacin Yobe to
    shi ya sa gwamnatin ta kafa wannan kwamitin don auna masu dauke da
    cutar da kuma su kan su masu lafiyar in Allah ya so matukar an kammala
    binciken aka kuma gano bakin zare to kuwa cutar ta koda za ta zama
    tarihi a jihar domin kuwa ba za mu dauki abin da wasa ba.
    Tambaya:- Yallabai me zai hana gwamnatin Yobe ta samar da wata
    cibiya ta musamman don kula da masu dauke da wannan cuta ta koda?
    Dokta:- A yanzu haka da nake magana cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin
    tarayya (FMC) da ke Nguru na da wata cibiya ta musamman da
    ke kula da masu dauke da cutar wadda gwamnatin Yobe da hannun ta cikin
    kafuwar  wannan cibiya ta Nguru don haka ashe ka ga muna da cibiya da
    ke kula da wannan cuta ta koda, kuma a nan Damaturu ma idan Allah ya so za
    mu yi kokarin samar da sashin da zai kula da masu dauke da wannan cuta
    a babban asibitin tunawa da marigayi Sani Abacha da ke Damaturu.
    Tambaya:- Ko gwammatin Yobe ta nemi wasu kungiyoyin ba da tallafi kan
    harkokin kiwon lafiya na kasa da kasa da na cikin gida dangane da
    wannan cuta?
    Dokta :- A gaskiya ba mu yi haka ba amma kuma shi taimako babu
    wanda ba ya so, don haka matukar in mun samu wani wanda ke sha\’awar
    taimaka wa bangaren ciwon oda ya nuna son taimakawa muna maraba da su.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here