MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
‘YAN sanda a Jihar Kuros Riba sun cafke wata mata mai suna Udoaka Sunday tare da wasu mutum uku da ake zargi da cin zarafin ‘yarta mai shekara 12 da haihuwa da take gayyato maza suna yin lalata da ‘yarta tana karbar kudi gurin su da kuma duk namijin da ta samu zai yi lalata da ‘yarta ta kama daga naira dubu 15.zuwa abin da ya fi haka gurin samarin yarinyar .
Wani makwabcin matar Udoaka ya bayyana wa wakilinmu na kudanci a sirrance cewa”ba ta dade da karbo naira dubu 15 ba wurin wani tsohon soja mai suna Effiom Okon, da ma wasu mutum hudu duk a zatonta ba a san abin da take yi ba tana bin samari da masu abin hannu tana karbar kudi hannun su tana hada su da ‘yarta suna lalata da ita”.
Majiyar labarin wannan jarida, ta ci gaba da cewa haka Udoaka take bin mutane musamman wadanda suke karbar kudin fensho tana karbe masu kudi tana tura ‘yar wurin su kuma ba tun yanzu take yin haka ba ta dade tana yi takan gargadi ‘yar da kada ta rika fashin zuwa wurin mutanen tana biya musu bukatar su.
Wakilinmu ya tambayi mahaifiyar yarinyar Udoaka Sunday yadda aka yi har aka fasa kwai sai ta ce “ Yarinyar ce da ta ga abin ya isheta sai ta gaya wa malamin su na makarantar boko ,shi kuma malamin ya sanar wa kungiyar kare cin zarafin yara kanana daga nan kuma suka sanar wa ‘yan sanda kwatsam ina zaune gida suka zo suka tafi da ni”inji ta.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Kuros Riba Irene Ugbo, ta tabbatar mana da labarin kana kuma ta ce tsohon soja Effiom Okon, da uwar yarinyar Udoaka Sunday, suna nan hannun su ana tsare da su.