Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN karamar hukumar Zuru Muhammed Kabir Abubakar, ya ja kunnen matasan Jihar Kebbi da na karamar hukumar Zuru baki daya na kula da kansu da kuma goya wa gwamna baya .
Ya yi wannan kira ne a yayin zantawarsa da manema labarai a Benin Kebbi inda
ya bayyana gamsuwarsa a game da tsarin mulkin Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu na sama wa matasa aikin yi a mai makon fadawa ayyukan ta\’addanci
na sara-suka da sace-sace , fyade, bangar siyasa da zama inuwa inuwa na kashe wando na babu gaira babu dalili.
Muhammed Kabir Abubakar ya ce gwamnan yashirya tsaf domin ganin cewa kowanne matashi ya dogara da kansa haka ya sa ya maida aikin namo dole ga kowa da kowa, da tilasta wa matasa karatu tun daga firamare har ya zuwa jami \’a, da koyan sana\’ar hannu.
Ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin jihar kebbi ta tanadi takin zamani tanasayar da shi akan kasa da farashin gwamnatin tarayya na naira 5500 da dari biyar Jihar Kebbi tana sayar wa da manoma a kan nairi 4000 dubu hudu domin saukaka masa, haka kuma gwamnatin tana biya wa dalibai kudin kammala jarabawar sakandare, tare da biya masu kudin jarabawar shiga jami\’a kyauta.