An Yi Hatsaniya Tsakanin Magoya Bayan Buhari Da Masu Son Ya Sauka A Kasuwar Wasai Da Ke Abuja.

0
763

Rabo Haladu Daga Kaduna

JAMI\’AN tsaro sun rufe kasuwar Wuse wadda ke babban birnin  Abuja, bayan wani yamutsi tsakanin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da masu goyon bayan ya sauka daga mulki.
Lamarin ya auku ne bayan yamutsi ya kaure tsakanin masu zanga-zangar, karkashin
jagorancin wani mawaki, Charley Boy da masu goyon bayan shugaban kasar.
Ahaji Usman Kamba wani dan kasuwa ne a Wuse, ya kuma shaidawa manema labarai  cewa, \”Al\’amarin ya faru ne da misalin karfe 10 zuwa 11 na safe, inda Charly Boy da tawagarsa suka fara ihun Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki in ba zai iya ba.\”
\”A lokacin ne su kuma Hausawa na cikin kasuwar suka fara ihun karya ne, karya ka ke
Charly Boy. Sai abin ya zama rikici har aka farfasa wa shi Charly Boy motocinsa.
\”Daga bisani sai \’yan sanda suka zo aka kori kowa aka rufe kasuwar,\” in ji mutumin.
Bayanai sun nuna cewa an lalata motocin Charly Boy da tawagarsa, har sai da ya sha da kyar. \’Yan sanda sun yi ta harbin iska don kawo doka da oda.
Kasuwar Wuse dai na daya daga cikin manyan kasuwannin da ke birnin tarayyar. Tun a watan Mayu da ya wuce ne dai shugaban kasar ya tafi London inda ake kula da lafiyarsa,
lamarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce a ciki da wajen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here