MAI MARTABA SARKIN FIKA A JAHAR YOBE YA KIRAYI SABABBIN DAGATAI 8 DA YA NADA DA SU ZAMA JAGORORI

2
1435
MUHAMMAD Sani Gazas Chinade, DAGA DAMATURU
MAI martaba sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan Jahas Yobe
Alhaji Abali Ibn muhammad Idris ya  kiirayi sababbin Dagatai da
Lamba-Lamba guda 8 da ya nada a masarautarsa da su zama jagorori
nagari abin kwatance ga na baya.
Mai martaba sarkin na Fika ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabin
gargadi ga sababbin dagatai da Lamba-Lamba da ya nada a masarautarsa
ta Fika da ke garin Potiskum a kwanakin baya.
Ya kara da cewar, a matsayinsu na jagororin al\’umma suna da rawar
takawa dangane da ci gaban yankunansu, don haka ya zama wajibi su
gudanar da mulki bisa adalci tare da samar da daidaito tsakanin
al\’ummominsu.
Daga nan sai ya neme su da su dukufa su da al\’ummominsu da addu\’ar
Allah (SWT) Ya ci gaba da bamu zaman lafiya a wannan yanki da Jahar
Yobe da ma kasa baki daya.
Da ya ke jawabi bayan nada shi a matsayin Lamban masarautar Farsawa
sabon Lawanin Alhaji Dahiru Malam ya godewa Mai martaba Sarkin na Fika
ne dangane da wannan mukami da ya ba shi tare bada tabbacin gudanar da
mulkinsa bisa adalci don tsira anan duniya da kuma kiyama.
Daga nan sai sabon Lamban ya nemi al\’ummar masarautarsa ta Farsawa da
su ba shi hadin kai da goyon baya don gudanar da mulkinsa bisa adalci,
domin da goyon bayansu ne zai samu damar sauke nauyin da Allah (SWT)
Ya dora masa.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here