AL’UMMAR KWAFTARA SUN GUDANAR DA AIKIN GYARAN GADARSU DA TA KUSA KARYEWA

0
756

  Isah  Ahmed, Jos

AL\’UMMAR garin Kwaftara dake karamar hukumar Lere a jihar Kaduna, sun gudanar da aikin gayya na gyara gadar garin da ta kusa karyewa a ranar Asabar din nan da ta gabata.

Da yake zantawa da wakilinmu a wajen aikin gyaran gadar shugaban kungiyar cigaban garin na Kwaftara, Alhaji Adamu Halilu ya bayyana cewa ganin yadda wannan gada ta lotsa da kuma yadda ruwa cinye gefan gadar wanda ya sanya ta kusa karyewa gabaki daya. Ya sanya al’ummar garin suka fito kwansu da kwarkwatarsu don aikin gyara gadar.

Ya ce a wannan aikin da muke yi muna son mu sanya buhunan yashi kamar 1500 don mu cike wajen da ruwa ya cinye a wannan gada.

 Ya ce wannan gada itace rayuwar  garinmu na  Kwaftara domin  ita ta hada mu da garin Saminaka.  

‘’Da wannan gada muke fitar da amfanin gonar da muke nomawa kuma da ita ne muke kai iyalanmu asibiti. Bayan haka  dubban manoman wannan yanki  suna amfani da ita wajen aikin gonakinsu da dibar kayayyakin amfanin da suke nomawa’’.

Alhaji Adamu Halilu ya yi bayanin cewa tuni wannan gada ta lotsa kuma  sun gabatarwa da  karamar hukumar Lere kukansu kan wannan matsala amma ba a sami damar zuwa a gyara mana wannan gada ba. Don haka ya yi kira ga gwamnati ta taimaka masu cikin gaggawa ta zo ta gyara masu wannan gada a yi masu wadda ta fi wannan tsayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here