AN DATSE WA WANI MATASHI KAI A KUROS RIBA

0
815
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  kalaba
FADAN kabilanci tsakanin kabilar Ediba dana Usumotong da ke kananan
hukumomin Abi da Yakurr ,jihar Kuros Riba, ya yi sanadin da wasu \’yan
ta,adda da ba ,a san  ko suwaye ne ba suka dauki fansa  sun yi wa wani
dan acaba maisuna Eric Omori Ewa, dan shekara 32, da haihuwa da ke
kauyen  Usumutong,karamar hukumar Abi jihar kuros riba yankan rago
suka datse masa kai suka tafi dashi .Lamarin ya faru ne bayan da
makisansa sukayi masa  kwanton vauna lokacin da ya  dauko wasu mata
uku a kan babur zai kaisu kasuwar Ugep,hedkwatar karamar  hukumar
Yakurr.
Makisan kamar yadda wata majiya ta shaida mana ana zargin daga kauyen
Ediba,suke suka tare hanyar da dan acabar ya taho wadda babu wata
hanya da ake bi musamman mutanen kauyen Usumutong, idan za su cin
kasuwar Ugep. Joseph Omini Ogburuwa, makwabcin wanda aka kashe ya
shaida wa wakilinmu na kudanci  a Kalaba cewa “Gwamnan al\’ummar  kauyen
Ebom,suka tare  hanya dana Ediba dauke da muggan makamai suka  tare
hanya  yana zuwa dai dai inda suke suka buge shi ya fado daga kan babur
din suka kashe shi suka cire masa kai suka tafi da shi,suka bar gangar
jikin matan kuma suka gudu saboda tsoron abinda ya faru ”.injishi
Daya daga cikin matan da aka harba a kafa  Peace  Enyieko, ta sanarwa
wakilinmu cewa ita da \’yar uwarta mai suna Juliet David Osim ,da
Ruth Osim Tom, da dan acaban ya dauko duk da sun gudu domin su tsira
da rayuwar su maharan sun bi su suka harbe su wata  a kafada wata a
baya  Sauran mutane da suka biyo hanya suka tsinakayi abin da ke gudana
daji suka rika yanka suna gudu domin su tsira  da rayukan su.
Wani mazaunin kauyen Ebom mai suna kwamared Ogburuwa,  ya ce  DPO. Mai
kula da ofishin \’yan sanda na Ugep Da abokin aikinsa DPO. Mai kula da
ofishin  Itigidi, karamar hukumar  Abi sun je kauyen  Usumutong,domin
gane wa idon su barnar da aka yi sun kuma ga gawar wadda aka datse wa
kai.Sun tabbatar wa a\’lummar Usumutong,cewa hedkwatar rundunar  \’yan
sanda ta Jihar Kuros Riba na bin kadin lamarin kisan da kuma matan uku
da aka sara.Kwamared Oguburuwa,yaci gaba da cewa duk da kasancewa
hedkwatar rundunar \’yan sanda ta gayyaci sarakuna da shugaban matasa
na Ediba su zo su yi mata bayani domin a zakulo makasan Ewa, lauyan
al,ummar Barista Essien  Andrew, ya  shiga cikin maganar ya nemi \’yan
sanda su yi wa mutanen Ediba hanzarin ba su lokaci su shirya zuwa gaban
,yan sandan domin su yi musu bayanin da suke nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here