ANA SA RAN FARFADO KAMFANIN MASAKA (KTL) DA KE GARIN KADUNA

0
724
Daga Usman Nasidi
KATAFAREN kamfanin samar da cigaba da yankin Arewacin Najeriya, NNDC tare da hadin gwiwar wata kamfanin kasar Turkiyya, SUR, zasu tayar da kamfanin masakar jihar Kaduna, wato ‘Kaduna Textile Limited (KTL).
Ana sa ran hadin gwiwar zata haifar da zuba jarin sama da dala miliyan 15 don sake raya kamfanin masakar data mutu tun shekarun baya.
Shugaban kwamitin sake farfado da kamfanin KTL, Alhaji Ali Gombe ya bayyana cewar kamfanin SUR ta nuna sha’awarta na zuba jari a wannan kamfani domin farfado da ita, tare da hadin gwiwar NNDC.
Majiyarmu ta jiyo Ali yana fadin, da zarar an cimma wannan yarjejeniya, ba da dadewa ba, kamfanin zata fara samar da kayayyakin Sojoji da ma na sauran kayan Sarki.
Ali ya cigaba da fadin alfanun sake farfado da kamfanin, inda yace yin hakan zai habbaka kasuwanci a yankin Arewa tare da inganta tattalin arzikin jihohin yankin, da ma na kasa gaba daya.
A tsarin yarjejeniyar, kamfanin SUR zata samar da kashi 35 cikin dari, yayin da sauran kason kudin zai fito ne daga jihohin Arewa 19 da gwamnatin tarayya, inji majiyarmu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here