Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
ILIMANTAR da al\’ummomin yankunan da ke fama da rikicin \’yan kungiyar
Boko-Haram kan sanin muhimmancin zaman lafiya da juna da illar kisan
kai a halin da ake ciki shi ne babban aikin dake kan wannan gwamnati
ta shugaba kasa Muhammadu Buhari.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin tsohon dan takarar shugabancin
kasar nan a tsohuwar jam\’iyyar PRP Alhaji Hassan Yusuf a tattaunawarsa
da wakilinmu dangane da bayanin da gwamnatin tarayya ta yi a kwanakin
baya cewar nan gaba kadan ake kyautata zaton dukanin \’yan gudin hijira
da suka rage za a mayar da su ga garuruwansu.
Ahaji Hassan Yusuf ya kara da cewar, ilimantar da al\’ummar yankunan da
da suka yi fama da tashe-tashen hankulan rikicin Boko Haram dangane da
muhimmancin zaman lafiya da juna da kuma illar kisan gilla shi ya
kamata gwamnatin tarayya ta dau himma akai kafin ma ta yi yunkurin
mayar da sauran \’yan gudin hijirar ga garuruwansu na asali da kuma
bayan an mayar da su ga garuruwansu.
Ya kara da cewar irin halin da aka shiga a wannan yanki dangane
rikicin Boko Haram inda aka rika yanka mutane da kona garuruwa
barkatai da farko dole ne da farko a ci gaba da addu\’a tare da
ilimantar da jama\’a illar yin hakan ta wajen nuna musu yin hakan
babban laifi ne a wajen Allah SWT.
Dangane da kudirin gwamnatin tarayya kuma na son mayar da sauran \’yan
gudin hijirar ya zuwa garuruwansu a cewar sa lalle wannan niyya tana
da kyau to amma gwamnatin za ta iya? Domin koda a halin yanzu in an
duba irin yadda \’yan gudin hijirar da ke kauyen Kukareta sama da dubu 20 ke zube
a filin Allah ba ishasshen ruwan sha ba wadataccen abinci da matsaguni
da sunan wai ana kula da su to ina ga kuma an mayar da su garuruwansu
ganin cewar an kona musu gidajen su kana ba su yi noma ballantana su
iya ciyar da kan su, to ai ka ga dole in tambayar anya kuwa gwamnatin
za ta iya?
Don haka ya zama wajibi matukar gwamnatin tarayya na son cimma wannan
kudiri nata na son mayar da sauran \’yan gudin hijirar ya zuwa
garuruwan su na asali to
akwai bukatar ta yi kyakkyawan shiri kan lamarin musamman ta wajen
gina musu gidajensu da samar musu abinci tare da ilmantar da su kamar
yadda na ambata a baya kana a kuma samar mu su da cikakken tsaro to
matukar an yi hakan to labudda kwalliya zata iya kaiwa ga biyan kudin
sabulu.