GWAMNATIN TARAYYA TA KASHE AKALLA NAIRA BILIYAN 6 WAJEN CIYARWA A MAKARANTU

0
649
Daga Usman Nasidi
MAHUKUNTA a fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari sun bayyana cewa gwamnatin su izuwa yanzu ta kashe kudi sama da Naira biliyan 6 a jahohi 14 na kasar nan domin ci da yara yan makarantan da suka kai kusa da muliyan 3 abinci mai rai da lafiya.
Mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa a harkar yada labarai Laolo Akande ne ya bayyana hakan ga manema labarai a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Majiyarmu ta samu daga gare shi cewa ya zuwa yanzu dai jahohin da suke cin gajiyar wannan shirin sun hada ne da na kudanci da kuma arewacin kasar kuma sune jihohin Anambra, Enugu, Oyo, Abia, Benue, Plateau, Bauchi, Osun, Ogun, Ebonyi, Zamfara, Delta Taraba da kuma Kaduna.
Haka nan kuma ya cigaba da cewa kafin shekarar nan kuma ta kare ana sa ran wasu karin jihohin za su anfana da shirin na gwamnatin tarayyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here