Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GTK ta samu tattaunawa da wani matashi dan kimanin shekaru 25 da
ke sana\’ar sayar da magungunan zamani Yusuf Muhammad Lamsha Potiskum a
Jahar Yobe wadda a yanzu haka ya mallaki kantunan sayar da magunguna
na zamani kemis guda biyu wadda ya ce sana\’ar sayar da magungunan
zamani ta yi masa komai na rayuwa.
GTK..Yaushe ka fara gudanar da wannan sana\’a taka ta sayar da
magungunan zamani (medicine), kuma ta yaya ka fara?
Lamsha..To alhamdulillah na fara sana\’ar sayar da magungunan zamani ne
tun a shekarar 2005 wato tun ina dan shekaru 15 ke nan kuma na fara ne
da kasa magungunan a cikin kwando ina yawo kwararo-kwararo daga
bisani kuma na fara zuwa kasuwanni.
Malam Yusuf ya kara da cewar, bayan da ya ga abubuwan sun fara bunkasa
sai ya zauna wuri guda tare da wani maigidansa Dr Muhammad mai
medicine a cikin tashar motar Potiskum yadda daga baya ya bude dan
wani karamin shago ya zuba magungunan ya na sayarwa ciki.
Ya ci gaba da cewar, ya na hakan ne sai Allah (SWT) Ya masa nasibi
jarinsa ya ci gaba da bunkasa ta yadda ya fita wajen tashar ya sayi
wani shago ya zuba magunguna a matsayin kantin sayar da magani kemis
ta yadda a duk sati sai ya je kano don sayo magunguna yana rarrabawa
wadanda ya ke hulda da su. Ana cikin hakan kuma ya kara sayan wani
shagon na biyu a cikin tsohuwar tasha ya sake zuba magunguna, abin sai
son barka.
GTK…Bayan kantuna biyu da ka bude, shin ko akwai wasu karin nasarori
da ka cimma da kake fahari da su akan wannan sana\’a?
Lamsha…Alal hakika na cimma karin nasarori na rayuwa da nake fahari
da su dangane da wannan sana\’a ta sayar da magunguna domin bayan
shagunguna biyu da na bude cike da magunguna na kuma gina gidan kaina
na yi aure na sa amaryar ciki kana na kan dauki kusan dukannin
dawainiyar iyalen gidanmu tare da biyan kudaden makarantar kannena
kuma ni kaina ma na dauki dawainiyar kaina da kaina yadda har na je na
yi karatun Diploma da ta yi sanadiyar samun aikin gwamnati da sauran
dawainiya ta \’yan uwa da abokan arziki dai-dai gwargwadon yadda zan
iya. Don haka a gaskiya wannan sana\’a ta sayar da magungunan zamani ta
yi min komai na rayuwa tabarkallah.
GTK…Da ya ke wannan irin sana\’a taku na bukatar kwarewa da neman
izini daga hukuma, shin ko kaima ka bi wannan mataki?
Lamsha…Alal hakika hukuma ta san da ni don kuma na samu izinin bude
kantunan sayar da magani daga gareta. Kuma batun kwarewa kuwa
alhamdulillah ina da dai-dai gwargwado.
GTK…Wane kira kake da shi ga masu wannan irin wannan sana\’a taka ta
sayar da magunguna musamman don bin doka da oda?
Lamsha…To ina kira da babbar murya ga \’yan uwana dake wannan sana\’a
ta sayar da magungunan zamani na gefen tituna da masu zama wuri daya a
kantuna da a guji ta\’ammali da sayar miyagun kwayoyin da gwamnati ta
hana da kuma kwayoyin da amfaninsu ya kare da wadanda basu da lambobi
da sauransu.