An Gano Kogi Mai Bangaren Ruwan Sanyi Da Na Zafi A Kuros Riba

0
809
AN gano wani kogi a garin Ugep hedkwatar karamar hukumar Yakurr, jihar
Kuros Riba mai abin al\’ajabi da ruwan kogin wani sashen sa ruwan dumi
wani kuma na sanyi wanda duk mutumin da ya shiga kogin wanka zai ji
haka.
Basaraken Ugep ,  Obol Ofem Ubana Eteng, ne ya sanar da haka
lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa.
Idan za,a iya tunawa a Nijeriya in banda ruwan da ke bulbulowa daga
kogin Ikogosi, jihar Ekiti wanda shima rabi ruwan sanyi rabi na dumi
har wanzu ba,a samu na biyunsa ba sai kwanan nan a Ugep.wakilin mu na
kudanci ya  tambayi basarake Obol Ofem Eteng,ko yaya ma akayi aka
gano ruwan  kuma waye nema har ya gano ruwan ya sanarwa masarauta sai
yace “wani mafarauci  ne dake yawon farauta ya gano shi ya kuma
garzayo ya sanar mana yaga wani kogi mai rabi ruwan sanyi rabinsa kuma
na dumi”.inji shi.
Wakilinmu,har wa yau  ya zanta da wasu da suka shiga kogin suka yi
kurme don gani da jin kwakwaf  yadda ruwan yake yawancin wadanda aka
zanta da su sun gaskata labarin sun ce tabbas babu karya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here