An Kiyasta Mutane Miliyan 60 Na Fama Da Rashin Ilimi A Duniya

0
689

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

AN bayyana rashin ko inkula a matsayin abin da ke haifar da matsalolin ilimin tarayyar Nijeriya.
Wani kwararre a kan harkokin ilimi da ke yin nazari a kan lamarin Alhaji Bello Kagara ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Kagara, ya ci gaba da cewa duk baki dayan lamarin ya faru ne sakamakon irin yadda shugabanni da wasu masu ruwa da tsaki ke nuna halin ko in kula a harkar ilimi.
Manazarcin ya ci gaba da bayyana yadda aka yi kan yadda za a lalubo hanyoyin ci gaban ilimi an bayyana wadansu alkaluma na jama\’a da ke fama da rashin ilimi da cewa akwai mutane akalla Miliyan 60 da ba sa zuwa makaranta a fadin duniya kuma daga cikin su akwai yara Miliyan 12 da kuma dimbin miliyoyin manyan da ba su iya rubutu da karatu ba, don haka lallai ana bukatar shugabanni su tashi tsaye ta yadda za a samu ingantacciyar nasarar a kasa da duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here