Miji, Matarsa Da \’Ya\’yansu 3 Sun Sheka Lahira Sanadiyyar Wata Shinkafa

0
746
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
WANI magidanci da matarsa tare da \’ya\’yansu uku shekaranjiya  sun
sheka lahira sanadiyyar cin shinkafa,wannan lamari kamar yadda
wakilinmu na kudanci ya samu labari ya faru ne a auyen Umuatuegwu,
yankin  Okija, karamar hukumar  Ihiala, jihar  Anambra .Al,amarin da
ya  jefa daukacin mutanen kauyen cikin firgici da damuwa.
Magidancin Albert Ndenemenu da matarsa mai suna Nwanne,  kamar yadda
muka samu labari tare da \’ya\’yan su uku sun gamu da ajalin su ne bayan
cin wata shinkafa da matar ta dafa musu shinkafa da matar Nwanne , ta
dafa musu matsayin kalaci bayan sun dawo daga aiki wata majiya da ke
makwabtaka  da iyalan da abin ya faru a akuyen  ta shaida wa \’yan
jarida cewa “bayan mutanen sun gama cin abincin jim kadan sai kowannne
su ya fara yin aman jini taba ka ta hanci suka rika faduwa kafin a yi
kokarin ba su agajin farko har a garzaya da su asibiti suka fara mutuwa
daya bayan daya”.inji majiyar haka dai mutanen biyar suka ce ga garin
ku nan.
Wani  makwabcin marigayi Albert da ya nemi  a sakaya sunansa ya ce
“da ma sana\’ar mutumin acava bayan da ya ga lokacin cin abincinsa na
rana ya yi sai ya dawo gida domin ya ci  abincinsa na rana, kamar
yadda ya saba , sun gama cin abincin kenan, jim  kadan sai suka fara
yin amai suna amayar da abincin hade da  aman jinni daga nan ne mu
kuma makwabta muka samu labari muka garzaya zuwa gidan domin ba su
agajin gaugawa kafin a tafi asibiti nan dai suka fadi daya bayan daya
suna mutuwa”.
Majiyar mu taci gaba da cewa “matar gabanta mijin da
\’ya\’yan uku suka mutu ganin haka ita ma ta yanke jiki ta fadi mace”.
Kwanan baya ma haka aka yi wasu iyalai a jihar Imo suma sanadin cin
shin kafa dafa duka suka mutu .Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar
\’yan sandan jihar Anambra Nkeiru Nwode,,game da lamarin ta ce tabbas
hakan ya faru amma suna nan suna gudanar da binciken sanadin mutuwar
ta iyalan biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here