AL\’UMMAR JAHAR YOBE NA NUNA DAMUWARSU KAN KASA GYARA MUSU HANYAR BAIMARI ZUWA GARIN NG

0
758
Muhammad Sani  Chinade, DAGA DAMATURU
AL\’UMMOMI da dama a Jihar Yobe na ci gaba da nuna damuwarsu dangane da
yadda babbar hanyar nan da ta tashi daga Bayamari zuwa garin Nguru a jihar ke ci gaba da kasancewa a lalace,yayin da hakan ke jawo yawan hadura da tsaikon zirga-zirgar
ababen hawa inda hakan yake shafar yanayin tattalin arzikin yankin.
Wannan hanyar mota dai hanya ce dadaddiya wacce ta shafe sama da shafe
sama da  shekaru 40 da gina ta wadda kuma ta ratsa kananan hukumomi 8
a jihar ta Yobe amma a zance da ake yi a yanzu babu wani dauki da
gwamnatin tarayya ta kawowa wannan hanya duk da irin muhimmancin da
take da shi ga harkokin tattalin arzikin yankin da ma kasa baki daya.
Kan hakan ne GTK ta samu zantawa da wani malami mai suna Baba
Sa\’idu Maijarida mazaunin garin Gashuwa dangane da irin wahalhalun
da suke fuskanta kan wannan hanya. inda ya kada baki ya ce,\”ga duk mai
bin wannan hanya tamu wadda ta taso daga kan iyakar mu da  jihar Jigawa zuwa Bayamari
dole ya ji tausayin jama\’ar wannan yanki namu, kuma duk inda ka taso a
cikin kasar nan babu inda ranka zai baci kamar wannan tsakanin sai ka
ce ba a Najeriya muke ba. Idan an kwatanta da wasu yankunan kasar nan.
Don haka shi a ganinsa a gaskiya gwamnatin tarayya ba ta yi wa wannan
yanki nasu adalci ba saboda ta mayar da su tamfar \’yan baya ga dangi ta
fuakar ayyukan raya kasa musamman ma hanyoyin mota \”.
Shi kuwa shugaba Bulakolo direba Koromari ya bayyana yadda sakamakon rashin gyara wannan hanyar yake shafar su,inda ya ce\”to gaskiya wannan hanya tana daga cikin hanyoyi
mafi muni a kasar nan kuma tana daya daga cikin abin da ke ci mana tuwo a kwarya domin duk kokarin ka ko sabuwar mota ka saya zaiyi wahala ta shekara lafiya bata lalace ba saboda  tsananin muninta. Sannan ita ma gwamnati ba ta gane abin yana shafarta domin tana da motocin sufuri
da ke bin hanyar amma idan ka bincika cikin shekara daya suke lalacewa\” .
Da GTK ke tuntubar kwamishinan ayyuka na jihar Yobe Alhaji Lawan Shettima kan ko me ake
ciki dangane da wannan hanya? Sai ya kada baki ya ce, \” wannan hanya
ce ta gwamnatin tarayya wadda kuma da dadewa ta bayar da ita gyara
daga Nguru zuwa Gashuwa ga kamfanin GYARAWA- sannan ta bai wa wani
kamfanin Chanis daga Gashuwa zuwa Bayamari, alhalin kuma su wadannan kamfanonin ba su
kammala ba sannan kuma ita gwamnatin tarayya ba ta soke kwangilar ba, saboda haka kaka babu yadda za a yi gwamnatin jiha ta hau kan aikin hanyar ba tare da an tabbatar cewa sun soke kwangilar da suka ba su ba\”.
Alhaji Lawan Shettima ya ci  gaba da cewa\”amma cikin \’yan kwanakin nan mun ba shi mai girma
Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam shawara kan ya tuntubi Ministan ayyuka na tarayya kan su matsawa wadannan kamfanonin kan su zo su ci gaba da aikin ko a soke kwangilar a ba wasu.\”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here