BUHARI GARKUWAR MUTANEN NIJERIYA NE-AMINU YAHAYA

    0
    778

    Isah Ahmed, Jos

    SHUGABAN kasuwar ‘yan tumatur dake farar gada a garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Aminu Yahaya Yunusa  ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari, garkuwar mutanen Nijeriya ne. Alhaji Aminu Yahaya Yunusa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan dawowar shugaban kasa, Muhammad Buhari daga jinyar da ya tafi waje.

    Ya ce Buhari  garkuwar mutanen Nijeriya ne, domin kafin zuwansa  Nijeriya ta shiga cikin wani mawuyacin hali musamman  a zamanin  gwamnatin da ta gabata.

    ‘’A kullum bama-bamai suna tashi a Nijeriya ana kashe daruruwan mutane. A wannan kasuwa kawai  mun sayi na’urorin  gano bama-bamai na  dubun naira  amma yanzu ga su nan mun ajiye su ba ma amfani da su’’.

    Alhaji Aminu ya yi bayanin cewa a gaskiya mun yi matukar farin ciki da dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari, a matsayinsa na shugaban kasa. Kuma za mu ci gaba da yi masa addu’ar Allah ya kara masa lafiya.

    Kuma muna kira kan ya ci gaba da abubuwan da  ya dauko tun da farko na maganar  tsaro da  noma da yaki da cin hanci da rashawa, domin sakamakon wadannan abubuwa da ya kawo yanzu Nijeriya tayi kyau. Babu shakka wadannan abubuwa suna da matukar alheri ga Nijeriya.

    Ya yi kira ga  al’ummar Nijeriya su ci gaba da baiwa shugaban kasa goyan baya da hadin kai kuma su  rungumi harkokin noma. Ya ce idan al’ummar Nijeriya suka rungumi harkokin noma maganar halin matsin da ake ciki za a warware shi.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here