GWAMNATIN JAHAR YOBE TA SAMAR DA GIDAJEN KWANA GA MALAMAN MAKARANTUN FIRAMAREN JAH

0
703
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GWAMNATIN Jahar Yobe ta gina gidaje ga maluman makarantun Firamare a
dukannin kananan hukumomin jahar 17 don samar da yanayin koyo da
koyarwa mai inganci a jahar.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin kwamishinan ma\’aikatar ilimin
Jahar Alhaji Muhammad Lamin a tattaunawarsa da GTK a ofishinsa da ke
garin Damaturu.
Kwamishinan ya kara da cewar,gwamnatin ta  aikata hakan ne a kokarin
da take yi na farfado da harkokin ilimi  daga tabarbarewar da ya yi
tare da karfafa wa malaman makarantun karfin gwiwar zuwa duk wurin da
aka tura su ba tare da taraddadin samun masauki ba musamman ma a
yankunan karkara.
Ya kara da cewar, a halin da ake ciki gwamnatin nada kyakkyawan
kudirin dangane da habaka ilimin \’ya\’ya mata wadda hakan na daga cikin
dalilan da suka sa suka fara samar da gidajen kwana ga malaman.
Alhaji Muhammad Lamin  ya ci gaba da cewar, jarin da gwamnatin jahar
ke zuba wa ga harkokin ilimi musamman ilimin sakandare ya fara samar
da kyakkyawan sakamako ganin cewar, daliban jahar da ke kammala
makarantun sakandare na samun sakamakon da ke kai su ga damar shiga
manya-manyan makarantun karo ilimi.
Don haka ya ba da tabbacin cewar gwamnatin za ta ci gaba  da ba da
gudummawarta ga harkokin ilimi don samar da kwararrun ma\’aikatan da za
su gudanar da harkokin jahar na yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here