SHIRIN BAI WA ‘YAN KASUWA RANCE YANA TAFIYAR HAWAINIYA A FILATO-HABIBU NALELE

0
657

Isah  Ahmed, Jos

MATAIMAKIN shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta karamar hukumar Jos da ke Jihar Filato Alhaji Habibu Lawal Nalele ya bayyana cewa shirin nan na bai wa kananan ‘yan kasuwar Nijeriya rance da gwamnatin tarayya ta kirkiro, karkashin bankin bunkasa masana’antu yana tafiyar hawainiya a Jihar Filato. Alhaji Habibu Lawal Nalele ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce akalla an yi wa kananan ‘yan kasuwa na karamar hukumar Jos ta arewa 3600 da suke bukatar wannan rance rajista, amma kashi 99 na wadannan yan kasuwa ba su sami wannan rance ba, har ya zuwa wannan lokaci.

Ya ce an yi alkawari cewa za a bai wa ‘yan kasuwar na jihar Filato  wannan rance tun a watan uku na wannan shekara, amma har yanzu da dama ‘yan kasuwar ba su sami wannan rance ba.

‘’A matsayinmu na shugabannin ‘yan kasuwa za mu iyakar kokarinmu wajen ganin cewa ba a sami wata matsala ba, kan wannan rance da za a bai wa ‘yan kasuwa. Ya  kamata a ce ya zuwa yanzu wannan rance ya isa hannun ‘yan kasuwa a dukkan kanannan hukumomi 17 da ake da su a Jihar Filato. Babu shakka  bai wa ‘yan kasuwar wannan rance zai farfado da harkokin kasuwanci a jihar Filato’’.

Don haka  kira ga  bankin  bunkasa masana’antu na Nijeriya, ya dubi yadda ake tafiyar da shirin baiwa ‘yan kasuwa rance a Jihar Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here