An Sami Rangwamen Farashin Raguna A Kalaba

0
896

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

AN samu rangwamen farashin dabbobi a kasuwar  ragunar  da ake sayarwa a kasuwar awaki ta Kalaba ,jihar kuros riba  Idan aka kwatanta da shekarar bara. Raguna suna yin sauki.Shugaban kasuwar Alhaji  Ishak Muhammad Hadeja  ne ya sanar da haka yayin hira da wakilinmu na kudanci.Yace “bana an samu saukin farahin raguna idan aka kwatanta su da shekarar bara,raguna sunayin sauki bana “.injishi

Dan kasuwar ya ci gaba da cewa “  shi lamarin rayuwa wata rana idan an samu tsanani wata rana kuma a samu sauki to wannan karo sauki ne Allah ya kawo mana kuma Alhamdulillahi mutane suna zuwa su saya duk da irin kukan rashin kudi da jama’a ke yi”.Ya kara da cewa a gaskiya yana jin bana kudanci ya fi arewa arha da kuma saukin sayen raguna musamman mu ana Kuros Riba.

Haka nan kuma ya kara bayyana saboda rahusa da ragunan ke yi masu saye domin layya ke zuwa ya ce “ farashi na kamawa daga Naira dubu 100 zuwa 80 ake sayarwa ,a bara kuma mun sayar da rago farashi Naira dubu 120 zuwa 130,ka ga bana an samu rangwame”.inji  Isyaka  Ruba. Dan kasuwar ya bayyana farin ckinsa game da janye musu masu masu karbar kudin rabanu da kuma haraji da jangali  da masu karbar ke ta kura musu suna zaluntarsu da kuma sanya su rika yin asara idan sun dauko dukiyar su zuwa kurmi domin sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here