MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
MAI horas da kungiyar wasan kwallon kafa ta babbar kotun Kano Barista Ibrahim Gwadabe ya ce gajiya ce da kuma rauni da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyarsa suka yi ne ya sanya kungiyar ba ta tabuka wani abIn a zo a gani ba a gasar wasan cin kofin babban mai shari’a na kasa wato CJ Cup da aka saba sanyawa kowace shekara, bana kuma aka yi hi a Kalaba Jihar Kuros Riba.
Barista Gwadabe, ya fadi haka ne zantawarsu da wakilinmu na kudanci a Kalaba jim kadan da kammala gasar ya ce” tun daga lokacin da aka sanya gasar cin kofin CJ Cup kungiyar mu ba ta taba zuwa kurar baya ba kamar wannan lokaci domin ko wace shekara mu ke zuwa na biyu muna kaiwa wasan karshe mu zo na biyu amma a bana sai ga shi a wasan kwara fainal aka fidda mu”inji shi.
Da aka tambaye shi me yake jin ya sanya dalilin waccan rashin nasara Barista Ibrahim Gwadabe ya ci gaba da cewa ‘yan wasanmu da yawa daga cikin su sun samu rauni wanda hakan nake ji shi ne ya haifar mana da koma baya da kuma rashin samun nasara yayin da ragowar ‘yan wasan kuma gajiya ce ta hana su tabuka komai”.Mai horas da kungiyar ya kara da cewa “tun a wasan kwata fainal aka fitar da mu wanda ba mu taba fuskantar rashin nasara kamar wannan lokaci ba.
Daga nan ya ce za su koma gida su sake daura damara domin tunkarar gasa ta badi .Daga nan ya gode wa ‘yan wasansa bisa kwazo da suka nuna yayin fafatawar, ya kuma jinjina wa shugabannin kungiyar da kuma babbar kotun Kano bisa goyon baya da kuma daukar dawainiyar kungiyar zuwa ko ina matukar dai an sanya gasar kowace shekara.