Sun Nemi Majalisar Dokoki Ta Kafa Dokar Cin Gashin Kai

    0
    790

    Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

     

    A ci gaban da daukacin kananan hukumomin tarayyar Nijeriya ke kokarin ganin sun samu ‘yancin cin gashin kansu a Jihar Neja ‘ya’yan kungiyar kananan hukumomi sun yi wani tattaki zuwa Majalisar dokokin jihar domin shawo kan ‘yan majalisar su saka wa dokar cin gashin kai hannu.

    A wannan gangami wani daga cikin shugabannin kungiyar Kwamared Abdullahi Aliyu,ya bayyana wa manema labarai cewa sun zo majalisar ne domin rokon arziki su saka wa dokar cin gashin kan hannu ta yadda za a samu yancin kai.

    Idan dai za a iya tunawa kananan hukumomin tarayyar Nijeriya sun shiga cikin wani mawuyacin hali ne sakamakon irin yadda Gwamnoni suka tauye kananan hukumomin ta hanyar yin asusun hadin gwiwa tsakanin jiha da majalisun kananan hukumomin.

    A hakikanin gaskiya dai wannan tsarin hadin gwiwa ya kashe majalisun kananan hukumomin baki daya ta yadda kamar yadda kowa ya sani a yanzu ba sa iya aiwatar da komai sakamakon halin babu da suka shiga ciki.

    Kodayake kamar yadda ‘yan magana kan ce idan bera da sata daddawa ma da wari saboda ana ganin dalilin da ya sa aka yi wannan tsarin ba ya rasa nasaba da irin yadda ake wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar jama\’ar kananan hukumomin a can baya.

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here