Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
KUNGIYAR teloli ta kasa reshen Jahar Yobe ta kaddamar da kwamitin
mutane 3 da za su rike harkokin kungiyar a matsayin riko na tsawon
lokacin da ba a ambata ba kafin gudanar da babban zabenta don ciyar
da kungiyar gaba.
Da yake jawabi ga GTK bayan da aka kaddamar da su a garin
Damaturu sabon shugaban rikon, Alhaji Ahmad Alhaji Modu ya ce, sun hada
wannan taro ne da zimmar hada kan mambobin kungiyar da yawansu ya
haura mutane dubu 10 a dukannin kananan hukumomin jahar 17 wadda sai
da hadin kai ne za su iya cimma muradinsu na ciyar da kungiyar gaba.
Shugaban rikon ya ci gaba da cewar, su masu gudanar da sana\’ar dinki
wato teloli sun gano cewar, babu yadda za su iya ci gaba ba tare sun
hada kansu ba kana su kuma samar da shugabanci nagari ta hanyar kungiya.
Ya kara da cewar, a fahimtarsu a halin da ake ciki babu yadda za a yi
masu sana\’a su samu tallafi daga gwamnati ko kuma wasu kungiyoyin ba da
tallafi ga masu sana\’a na cikin gida da na waje ba tare da kungiya ba.
Alhaji Ahmad Modu ya kara da cewar, a halin da ake ciki mambobin
kungiyarsu ta telolin Jahar Yobe ta zabe su, su uku a matsayin
shugabannin rikon da za su gudanar da harkokin kungiyar kafin gudanar
da zabe, wato an zabe shi a matsayin shugaban riko sai kuma matsayin
sakatare an bayar ga Malam Gana Katarko sai kuma matsayin ma\’ajin kudi
aka bayar ga Musa Ahmad Potiskum.
Don haka shugaban rikon ya roki gwamnatin Jahar Yobe da ta tallafa
musu da karin kekunan dinki irin na zamani ko da ma bashi ne ganin
cewar kungiyarsu ta teloli kungiya ce da ke sahun gaba ta bangaren
samar wa da matasa aikin yi. Domin in da za a kiyasta kungiyarsu akalla
takan iya yaye matasa masu koyon sana\’a sama da dari 4 a duk shekara.
Daga nan sai ya nemi mambobin wannan kungiya ta su da su zama masu ba
su goyon baya don ganin sun tafiyar da jagorancin da suka dora musu
bil-hakki da gaskiya don cimma kudirin da suke bukata na inganta
kungiyar da rayuwar membobinsu.