AN CAFKE WANI UBAN DA YA YI WA \’YARSA FYADE HAR SAU 3 A JIHAR KANO

0
873

Daga Usman Nasidi Da Rabo Haladu

RUNDUNAR \’yan sandan Jihar Kano ta koka kan yawaitan samun iyayen da ke zakkewa \’ya\’yansu ta hanyar fyade a Jihar Kano.

Kakakin rundunar \’yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majia ya bayyana wa \’yan jaridu cewar wannan wani sabon laifi ne wanda ba su taba tunanin afkuwarsa ba.

DSP ya bayyana cewa “Mun kama wannan mutumi ne a Unguwa Uku, wanda ya yi wa \’yar cikinsa \’yar shekara 14 ciki, kuma ana zubarwa har sau 3.”

Hakazalika Majia ya bayyana wani mutum da suka taba kama wani mutumin banza da ya yi wa \’yan mata su uku fyade, kuma dukkaninsu \’yan gida daya.

Bugu da kari sun kama wani mutumi da yake yi wa wata \’yar uwarsa fyade ba sau daya ba sau biyu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here