Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
YA zama wajibi mu ci gaba da gyara halayyar al’umma musamman ma mutanen da suka kammala zaman gidan jarun da zarar sun samu kansu don su zama mutane nagari da za su ba da gudummawarsu ga ci gaban kasa.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga sakatariyar hukumar da ke kula da bibiyar da gyara halayyar al’umma don sake inganta su da ke jahar Yobe Barista Hadiza Alkali a tattauanwarta da wakilinmu a garin Damaturu.
Sakatariyar ta ci gaba da cewar, dangane da kokarin cimma wannan kudiri na su ne ma hukumar su ta samar da wassu cibiyoyin sake inganta rayuwar al’umma guda uku a garuruwan Potiskum da Nguru da kuma garin Gashuwa musamman don mutanen da suka yi zaman gidan jarun a jahar da nufin sake sa su a hanyar da za su samu damar gyara halayensu ta yadda za su zama mutane nagari nan gaba.
Ta ci gaba da cewar, bayan wadancan cibiyoyin gyaran halayyar jama’a guda uku da aka kafa har ila yau shirye-shirye sun yi nisa wajen sake gina wadansu karin cibiyoyin guda uku a garuruwan Fika da Gaidam da kuma Dapchi a karamar hukumar Bursari.
Barista Hadiza Alkali ta kara da cewar, wannan hukuma ta su ta dukufa matuka wajen ganin ta gyara halayyar mutanen da suka yi zaman gidan yari ne ba don komai ba sai don ganin yin hakan shine babbar fa’ida ga jahar da ma kasa baki daya domin kuwa matukar an bar su kara zube da yawa-yawansu kan iya komawa ‘yar gidan jiya ta yadda za su zama babbar barazana ga al’umma duk da cewar da yawan wadanda suka yi zaman gidan jarun din kaddara ne ta kai su ga hakan amma ba wai don sun cancanta da hakan ba.
Ta ci gaba da cewar, a kokarin su na wajen ganin sun inganta rayuwar wadanda suke zaman gidan yari a watan Ramadan da ya shude hukumar su ta samar da kayayyakin shan ruwa da makamantansu ga ’yan jarun din da ke wassu gidajen yarin jahar. Don haka ta godewa gwamnan jahar dangane da goyon bayan da ya ke ba su.