KAMFANIN IRIN SHUKA NAMASLAHA YA SHIRYA RANAR MANOMA A KARAMAR HUKUMAR LERE

    0
    835

    Isah  Ahmed, Jos

    KAMFANIN irin shuka na Mashala da ke tallafa wa manoma da rancen irin shuka da takin zamani ya shirya ranar manoma a wata babbar gona da ke kauyen Gidan Dutse a karamar hukumar Lere da ke Jihar Kaduna.

    Da yake jawabi a wajen taron mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana cewa aikin noma ne kadai zai inganta Nijeriya da kasashen Afrika baki daya.

    Ya ce babu abin da zai  taimaki talakan Nijeriya  kamar noma, kuma babu wani taimako da za a yi wa manoman Nijeriya kamar  a samar  masu da irin shuka ingantatce  da takin zamani kan farashi mai rahusa.

    Ya ce babu shakka al’ummar karamar hukumar Lere sun rungumi aikin noma musamman noman masara, don haka yankin ya shahara a duniya.

    Ya yaba wa wannan kamfani na Maslaha kan yadda yake samar wa da manoma irin shuka ingantatce. ‘’Wannan kamfani  yayi rawar gani a Nijeriya da kasashen Afrika wajen samar wa da manoma ingantatcen irin shuka. Don haka muna godiya ga wannan kamfani kuma muna tabbatar wa  kamfanin cewa  za mu ci gaba da rike shi.  Domin irin nasarar da ya kawo  karamar hukumar Lere zai taimaka  wajen bunkasa noman masara a  yankin da Jihar Kaduna da kasa baki daya’’.

    Ya yi kira ga kamfani ya kara kirkiro wasu irin shuka na wasu kayayyakin amfanin gonar da manoma za su yi amfani da su wajen bunkasa harkokin nomansu.

    Daga nan ya yi  kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin arewa su tallafa wa wannan kamfani na Maslaha Seeds.

    Shi ma a nasa jawabin wani babban manomi a yankin da aka yi wannan biki a gonarsa, Alhaji Abdul’azeez Gidan Dutse ya bayyana cewa yana da manyan gonaki guda 12 amma ada noman  ya so ya gagare shi. Ya ce  amma da taimakon Allah da ya kawo  wannan kamfani  a daminar bana, suka ba shi irin masara da takin zamani  ya yi noman da ban taba yin irinsa ba, wajen yawa da kyau.

    Ya ce a  wannan gona da ake yin wannan biki a cikinta  a da yana sanya mata buhunan taki guda 300 amma a daminar bana ya sanya mata taki buhu 125 kawai,  saboda amfani da ya yi da  irin shuka na wannan kamfani.

    Ya ce a da a duk shekara ya kan yi buhu 1500 na masara a wannan goma, amma a bana bai san irin dubban buhunan da zan yi ba, sakamakon kyawon da wannan gona ta yi.

    A nasa jawabin shugaban kamfanin na Maslaha Seeds Sanata Sa\’idu Muhammad Dansadau ya bayyana  cewa babban burin wannan kamfani shi ne bunkasa harkokin noma a Nijeriya, domin a bunkasa kasar da abinci da

    wadata masana’antu da kayayyakin amfanin gonar da za su rika sarrafawa da kuma  daukar masarar da manoma suka noma a fitar zuwa kasashen waje.

    Ya ce wannan kamfani  shi ne  na daya a Afrika ta Yamma wajen samar da ingantatcen irin shuka.

    Ya ce kwararru kan aikin noma sun tabbatar da cewa yankin Saminaka ne kan gaba a aikin noma a Afrika ta Yamma. Don  haka wannan kamfani ya zo yankin domin ya yi aiki tare da manoman  yankin wajen bunkasa harkokin noma a Nijeriya.

    A nasa jawabin wakilin kamfanin a karamar hukumar Lere Alhaji Umaru Haidanu Ibrahim Saminaka ya bayyana cewa manoman wannan yanki sun yi amfani da eka 4000 ne na wannan shiri a daminar bana.

    Ya ce a cikin manoman da suka shiga wannan shiri akwai manoman da aka bai wa taki tirela uku da buhu 124 rance akwai wanda aka bai wa taki tirela biyu akwai wanda aka bai wa taki tirela daya.

    ‘’Babu ko kwabo da wani manomi ya biya kafin mu bashi wannan rance. Manoman sun kawo mana katin dan kasa ko katin zabe ne kawai muka je muka gwada gonakinsu muka basu wannan rance. A kowace eka muna bai wa manomi buhun taki 6 da irin masara. Idan kaka ta yi manomi zai biya da wannan masara da ya noma. Kuma babu ruwa a wannan rance,  abin da aka bai wa manomi haka zai biya. Ya zuwa yanzu duk manoman da suka shiga wannan shiri suna ta godiya ganin ingancin irin masara da takin  da aka ba su. Suna cewa za su ninka abin da suke nomawa a shekarun baya.’’

    Shi dai wannan biki na ranar manoma da wannan kamfani ya shirya, ya sami halartar kwararru kan kan harkokin aikin noma daga jama’ar Ahamdu Bello da ke Zariya da manoma daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna, jihohin Kano da Bauci.

     

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here