ZA MU YI WA DIEZANI MUMMUNAR KAMU IDAN BUHARI NE KAN MULKI

0
780

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar nan tu\’annati da zagon kasa wato Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sha alwashin sai ta kamo tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya kuma ‘yar gaban goshin Goodluck Jonathan ta kuma yi mata hukunci.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin Sakatarenta Mista Emmanuel Aremo lokacin da ya tarbi wata tawagar masu zanga-zanga a babban ofishinsu da ke a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Majiyarmu ta samu labarin cewa masu zanga-zangar wadanda wannan mawakin mai suna Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy shi ne ya jagorance su inda kuma suka bukaci da a gaggauta maido ta cikin kasar nan domin ta fuskanci hukunci.

To sai dai Sakataren hukumar ta EFCC ya shaida wa masu zanga-zangar cewa suna nan suna aiki ba dare-ba-rana domin ganin an maido da ita Najeriya kuma inda shugaba Buhari ne ke mulki, to su sha kurumin su hakan za ta faru.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here