Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
TSOHON dan majalisar dattawan kasar nan mai wakiltar kudancin Jihar
Yobe a majalisa ta 7 da ta shude Sanata Alkali Abdulkadir Jajere ya
bayyana kudirin na amsa kiran al\’ummar matukar sun sake nemansa don
wakiltarsu a majalisa ta 9 mai zuwa a zaben da ke tafe a shekarar 2019.
Dan majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da
wakilinmu a garin Damaturu dangane da
yadda yake ga ake tafiyar da shugabancin majalisa ta 8 a karkashin
shugabancin Abubakar Bukola Saraki.
Alkali Abdulkadir Jajere ya ci gaba da cewar yadda yake ganin a
halin yanzu ake gudanar da shugabancin majalisa ta 8 abin a yaba ne
musamman in an yi la\’akari da cewar jam\’iyyarsu ta APC ita ce ke da
rinjaye a majalisar sabanin a majalisar da ya taka rawa cikinta daga
shekarar 2011 zuwa shekara ta 2015 wato majalisa ta 7 wacce a wancan
lokacin jam\’iyyar PDP ce ke jagorantar ta.
Sanata Jajere ya ci gaba da cewar, in an lura majalisar dattawan kasar
nan da kuma \’yan uwansu na wakilai suna ayyukansu daidai wa daida ta
yadda suke kokarin samar da dokokin ciyar da kasa gaba kamar yadda
jajirtaccen shugaban kasarmu Muhammadu Buhari ke da shi. Illa \’yan
kurakure \’yan kalilan da ba a rasa ba wadanda muke fatan za su gyara
yadda zai zo daidai da bukatun talakawan kasar nan da su ne suka yi
tsayuwar daka da ya yi sanadiyyar zuwan wannan gwamnati mai adalci cikin
ikon Allah.
Dangane da na\’amta don sake tsayawa takarar kujerar dan majalisar
dattawa a mazabar kudancin Yobe in har al\’ummarsa sun neme shi a kan
hakan. Jajere ya ce lalle a shirye yake da ya amsa kiran jama\’ar
matukar sun neme shi kan hakan domin ai na ji dadi shi ne gari ba na
saba ba.
Jajere ya ci gaba da cewar, shi ya hakkake cewar a halin da ake ciki
al\’ummar mazabar sun gane cewar lalle lokacin da yake wakiltarsu a
majalisa ta 7 sun samu wakilci nagari sabanin yadda suke a yanzu.
Don haka ya ba da tabbaci ga al\’ummar mazabarsa kan cewar, a shirye yak
da ya sake tsayawa don wakiltarsu matukar sun bukace shi a kan hakan.
Alkali Jajere ya kuma yaba wa Gwamna Ibrahim Gaidam na Yobe dangane da
yadda yake gudanar da ayyukansa bil-hakki da gaskiya musamman dangane
da ayyukan raya kasa da yake aiwatar a dukannin sassan jihar.