TABARBAREWAR TSARO LAIFUKAN HANNAYENMU NE – IMAM ISAH

0
843
Muhammad Sani  Chinade, DAGA DAMATURU
AN hori al’ummar musulmi da su ci gaba da gyara halayensu
gami da addu’ar neman Allah (SWT) da ya kawo musu dauki dangane da
halin tabarbarewar tsaro da ke addabar yankunansu.
Wannan nasiha gami da kiran sun fito ne daga bakin babban limanin jumu’a na masallacin
rukunin gidajen Shagari da ke garin Damaturu Ustaz Yakubu Isa a cikin
hudubarsa ta sallar jumu’a da ya gabatar a makon da ya gabata hudubar
da akasari ta kunshin bayani kan halin da al’ummar musulmi ke
ciki na rashin tsaro musamman a yankunan jahohin Yobe da Borno da kuma
Adamawa da kuma sauran yankunan arewacin kasar nan.
Babban limamin jumu’a din ya kara da cewar lalle al’ummar musulmi su dauka kan cewar irin
wannan hali da ake ciki da farko su dauke shi a matsayin kaddara daga
Allah (SWT) kana su kuma dauka kan cewar saba wa
Mahalicci Allah (SWT) ma kan iya sa a samu kai cikin wannan irin jarrabta.
Don haka lalle akwai bukatar da a dukufa wajen addu’ar tuba
ga Allah (SWT) tare da rokon sa kan ya fitar da mu daga cikin halin da
muke ciki dangane da tabarbarewar tsaron da ya ke barazana ga
samun nutsuwar ci gaba da gudanar da addinin mu da sauran harkokin rayuwar mu na yau da kullum.
Ya kuma bayyana cewar akullum addinin musulunci na koyar da mabiyansa
yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau tare da yin hakuri da juna a kowace hanya ta mu’amallat da kuma zama ma su yafiya ga juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here